Kwana 4 a tsare: Ibrahim Magu ya bukaci a basa beli ya tafi gida

Kwana 4 a tsare: Ibrahim Magu ya bukaci a basa beli ya tafi gida

- Zargin amsan N4bn hudu daga hannun Magu, Osinbajo ya kai kara wajen IG na yan sanda

- Manyan Diraktocin EFCC 16 sun gurfana gaban kwamitin bincike

- Lauyan Magu ya ce ana take masa hakkinsa na dan Adam ta hanyar tsareshi

Mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, ya bukaci beli daga kwamitin fadar shugaban kasa dake bincikensa.

Magu ya yi kwanansa na hudu a hedkwatar sashen binciken yan sanda FCID.

Ya kasance hannun jami'an yan sandan FCID tun ranar Litinin da aka yi awon gaba da shi zuwa fadar shugaban kasa.

Kwamitin Fadar shugaban kasan na binciken Magu ne kan tuhume-tuhumen da Ministan Shari'a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami, yayi masa.

Hakazalika ranar Alhamis, wasu manyan ma'aikatan EFCC da NFIU 16 sun gurfana gaban kwamitin karkashin jagorancin Alkali Ayo Salami.

Daga cikin manyan ma'aikatan akwai Sakataren EFCC, Ola Oloyede; Diraktan ayyuka, Mohammed Umar, da kuma CP Bolaji Salami.

Majiyar The Nation ta bayyana cewa: "Kwamitin ta baiwa ma'aikatan EFCC mako daya su gabato da jerin bincike-binciken da suka yi tun shekarar 2015."

Kwana 4 a tsare: Ibrahim Magu ya bukaci a basa beli ya tafi gida
Kwana 4 a tsare: Ibrahim Magu ya bukaci a basa beli ya tafi gida
Asali: Twitter

Bincike ya nuna cewa Lauyoyin da ke tsayawa Magu sun bukaci belinsa.

Sun roki kwamitin ta yiwa Sifeto Janar na yan sanda magana ya saki Magu bisa beli saboda hakkinsa ne na dan Adam.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wani dan majalisa daga Legas ya mutu

Wata majiyar The Nation ta bayyana cewa: "A zaman da kwamitin tayi, Lauyan Magu ya bukaci beli. Amma tunda kwamitin ta yi ikirarin cewa ba ita ta ce a tsareshi ba, an shawarci lauyoyin su mika bukatarsu Ga Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu."

Lauyan ya ce "Bayan kasancewa hakkinsa na dan Adam, muna bukatar a baiwa Magu beli saboda babban jami'in dan sanda ne."

"A barikin yan sanda ya kamata a tsareshi har a kammala binciken ba cikin kurkukun yan sanda ba."

"A ranarsa na farko a FCID, kan kujera ya kwana har wayewar gari. Ya bukaci su kaishi cikin Cell amma aka ce sai dai ya kwana a Ofishi. Amma saboda tsaro, ya zabi kwanciya kan kujera."

"Magu na gurfana ne gaban kwamitin bincike, babu wata hujjar tsareshi."

Bayan jawabin Lauyoyin, majiyar ta bayyana cewa an bukaci Magu da masu tsaya masa su fita daga dakin na dan mintuna.

Amma basu yanke shawara kan bukatar belin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel