Mumunan harin kwantan bauna: Yan Boko Haram sun kashe Sojoji 20

Mumunan harin kwantan bauna: Yan Boko Haram sun kashe Sojoji 20

Akalla Sojojin Najeriya Ashirin (20) sun rasa rayukansu yayinda saura da dama suka jikkata yayinda wasu yan ta'addan Boko Haram suka kai harin kwantan bauna jihar Borno ranar Talata.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sojojin sun hallaka yan ta'addan Boko Haram 20 a musayar wutan.

An tattaro cewa harin ya auku ne a hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ana saura kimanin kilomita 30 da garin Damboa.

Majiya daga gidan Soja ya laburtawa mai rahoton DT cewa yan ta'addan sun budewa Sojoji wuta ne kuma hakan yayi sanadiyar mutuwar Soji da dama.

Yace: "Abin da ban takaici, Dakarunmu sun je sintiri kuma yayinda dawowansu Damboa, kimanin kilomita 30, sai yan ta'addan suka bude musu wuta ta ko wani hanya."

"Mun yi asaran fiye da Sojoji dozin."

"An kai gawawwakin Sojin da suka mutu Maiduguri tare da wadanda suka jikkata."

"Yanzu haka suna jinya a wani asibitin Sojoji,"

Mumunan harin kwantan baunan: Yan Boko Haram sun kashe Sojoji 20
Yan Boko Haram sun kashe Sojoji 20
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin siyasar APC ya dau sabon salo a Ondo, an dakatad da mataimakin kakakin majalisa

Amma hukumar Soji ta ce Sojoji biyu kadai aka kashe.

Rundunar ta sanar da cewa, a wani kicibus da ta yi da mayakan Boko Haram a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, 'yan ta'adda 17 sun bakunci lahira.

Haka zalika ta sanar da cewa, wasu da dama daga cikin 'yan kungiyar masu tayar da kayar bayan sun tsere da raunuka daban-daban na harbin harsashi.

A yayin jaddada gagarumar nasarar da dakarun sojin suka samu yayin wannan artabu a ranar Talata, an kuma tsinto miyagun makamai da mayakan suka zubar yayin neman ta kansu.

Da ya ke karar kwana babu inda ba ta kai ziyara, rundunar sojin kasan ta yi rashin sa'a yayin da wasu dakaru biyu suka sadaukar da rayukansu wajen kare martabar kasar nan.

Haka kuma wasu dakarun hudu sun jikkata yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram a filin daga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel