Tsakani na da wanda aka kama yana cusa Dala a aljihu, wa ya kamata a killace - Wike ya yiwa Ganduje raddi

Tsakani na da wanda aka kama yana cusa Dala a aljihu, wa ya kamata a killace - Wike ya yiwa Ganduje raddi

Shugaban kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na jihar Edo, Gwamna Nyesom Wike, ya mayarwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, martani.

Wike ya ce barazanar da takwararsa na jam'iyyar All Progressives Congress APC ke yi na nuna cewa sun shirya amfani da jami'an tsaro wajen murde zabe.

Ganduje ne shugaban kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC na jihar Edo.

Za'a gudanar da zaben gwamnan Edo ranar 19 ga Satumba, 2020.

A ranar Litinin, Ganduje ya lashi takobin cewa APC zata ci mutunci Godwin Obaseki a Edo ta hanyar killace Wike.

Rahoton Shi kuma Wike a martaninsa, ya ce mutumin da aka kama yana cusa dala cikin malin-malin ya kamata a killace, Sahara Reporters ta ruwaito.

Yace: "Tsakani na da mutumin da aka gani yana cusa Dala cikin aljihu, wa ya cancanci a killace?"

Tsakani na da wanda aka kama yana cusa Dala a aljihu wa ya kamata a killace - Wike ya yiwa Ganduje raddi
Wike ya yiwa Ganduje raddi
Asali: UGC

KU KARANTA: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam'iyyar PDP na harin tarin dukiyar asusun jihar Edo ne, shiyasa take goyon bayan Gwamna Obaseki.

Ya yi alkawarin cewa, nan da ranar 19 ga watan Satumba, "Gwamna Obaseki zai tozarta yayin da za a killace Gwamna Wike".

Ganduje wanda ya zanta da manema labarai jim kadan bayan rantsar da 'yan kwamitin kamfen dinsa, wanda kwamitin shugabanci rikon kwarya karkashin Gwamna Mai Mala Buni suka yi a babban ofishin jam'iyyar a Abuja, ya ce nasara na tare da APC.

Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC zai kara da Godwin Obaseki na PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel