Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da Ibrahim Magu, matsayin shugaban EFCC

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da Ibrahim Magu, matsayin shugaban EFCC

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa fadar shugaban kasa ta dakatad da Ibrahim Magu matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC, BBC ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da Ibrahim Magu, matsayin shugaban EFCC
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da Ibrahim Magu, matsayin shugaban EFCC
Asali: Depositphotos

Mun kawo muku rahoton cewa mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.

Da misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ta kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami'an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa.

Tuni Majiya ta bayyanawa The Nation cewa da wuya Magu ya tsira daga dakatad da shi.

"Hanashi komawa ofishinsa alama ce dake nuna cewa za'a dakatad da shi.

"Ya bayyana karara cewa fadar shugaban kasa ta kammala shirin neman sabon wanda zai maye kujerar." Cewar Majiyar.

Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu

1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati

2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn

3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya

4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya

5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu

6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn

7. Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace

8. Fifita wasu jami'an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da 'Magu Boys'

9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba

10. Sayar da dukiyoyin sata ga yan'wansa, abokan arziki da abokan aiki

A ranar Litinin, an gayyace Ibrahim Magu, fadar shugaban kasa domin amsa tambayoyi da wasu tuhume-tuhume da ake yi masa kimanin 22.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel