Bayan kokarin baro jirginta, Majalisar dinkin duniya ta dakatad da kai tallafi Arewa maso gabas

Bayan kokarin baro jirginta, Majalisar dinkin duniya ta dakatad da kai tallafi Arewa maso gabas

Majalisar dinkin duniya ta dakatad da kai agaji da tallafi a jirgin sama sakamakon yunkurin da akayi na baro jirginta mai saukar Angulu a jihar Borno.

Wannan ya biyo bayan ruwan harsasan da yan Boko Haram masu yunkurin shiga garin Damasak suka kai wa jirgin majalisar dinkin duniya a ranar Alhamis.

Shugaban shirin tallafi da bada agaji na majalisar dinkin duniya dake nan Najeriya, Edward Kallon, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Asabar, Daily Trust ta bayyana.

Edward yace: "Duk da cewa har yanzu muna duba abinda ya faru, mun tabbatar da cewa akwai alaman harbin harsasai jikin daya daga cikin jirage mai saukar angulu yayinda ta nufi Damasak."

"Jirgin ta samu nasarar juyawa kuma ta koma Maiduguri. An ci sa'a babu wanda ya ji rauni cikin matukan jirgin, kuma babu fasinjoji ciki a lokacin."

"Amma, dubi ga irin hadarin abinda ya faru, kuma bisa shawarar UNDSS da UNHAS/WFP, ina mai dakatad da shirin agaji da jinkan UNHAS a Arewa maso gabas, domin bamu daman tattaunawa da gwamnati wajen duba tsaron jiragenmu da kuma ganin yadda za'a kiyaye gaba."

Edward Kallon ya ce wannan dakatarwan na tsawon makon daya ne. Bayan mako daya za'a sake duba lamarin.

Ya ce cikin mako dayan, agajin gaggawa da kwashe wadanda rayukansu ke shirin hadari zai kasance daya-daya ne kuma da umurnin shugaba.

Shirin lamunin abincin duniya WFP ke gudanar da sufurin jirgin saman domin taimakawa wajen safarar ma'aikatan kungiyoyin tallafi da jinkai zuwa wurare masu hadari kuma kan farashi mai sauki.

Hakazalika jiragen na taimakwa kai agajin gaggawa ga wadanda hari ya rutsa da su.

Bayan kokarin baro jirginta, Majalisar dinkin duniya ta dakatad da kai tallafi Arewa maso gabas
MDDuniya
Asali: UGC

Legit ta kawo muku rahoton cewa an bude wa wani jirgi mai saukan ungulu mallakar Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) wuta a Damasak, a karamar hukumar Mobbar da ke arewacin jihar Borno.

Duk da haka, jirgin ya lallaba ya dawo sansaninsa a Maiduguri jim kadan bayan harin da aka kai masa a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020.

UNHAS na taimakawa ne wurin rabon abinci da karkashin shirin samar da abinci na duniya a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel