Matar gwamnan Benue da ɗansa sun kamu da cutar korona

Matar gwamnan Benue da ɗansa sun kamu da cutar korona

Eunice Ortom, matar gwamnan jihar Benue, ta kamu da kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Matar gwamnan da fitar da sanarwar hakan a daren ranar Juma'a inda ta ce dan ta da wasu maaikatanta suma sun kamu da cutar.

Ta shawarci dukkan wadanda suka gana da ita a baya bayan nan su killace kansu kuma su tafi ayi musu gwajin na COVID-19.

Eunice ta ce kamuwa da cutar baya nufin mutum zai mutu tare da cewa tana fitar dan ta da ita za su warke.

Matar gwamnan Benue da ɗansa sun kamu da cutar korona
Matar gwamnan Benue da ɗansa sun kamu da cutar korona. Hoto daga The Nation
Asali: Depositphotos

"A daren yau, na samu sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta yi min a kamar yadda aka saba yi a gidan gwamnati a Makurdi kuma sakamakon ya nuna ni da da na da wasu maaikata na mun kamu," a cewar sanarwar.

KU KARANTA: Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai – Majiya daga Rundunar Soji

"A halin yanzu mun killace kan mu kamar yadda kaidar cutar ta ke kuma za mu fara shan magunguna a karkashin kulawar likitoci.

"Duk da cewa na kira dukkan wadanda na san na yi cudanya da su na fada musu su tafi gwaji, ina shawartar duk wanda ya yi cudanya da ni cikin makonni biyu da suka gabata ya tafi a gwada shi.

"Ina son tunatar da mutane cewa COVID-19 ba ya nufin mutuwa duba da adadin mutanen da ke warkewa kawo yanzu saboda haka kowa ya kwantar da hankalinsa amma akwai bukatar mu cigaba da kulawa.

"Ina shawartar mutane su cigaba da kiyaye kansu da bin dokokin hukumomin lafiya. Ku kasance lafiya! COVID-19 gaskiya ne!."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel