Rayuwata ta sauya tunda matata ta fara hana ni hakkina - Magidanci

Rayuwata ta sauya tunda matata ta fara hana ni hakkina - Magidanci

- Wani magidanci mai suna Abidemi Dada ya roki wata kotun gargajiya da ke zama a Ibadan da ta tsinke aurensu da matarsa mai shekaru 13

- Injiniyan ya tabbatar wa da alkalin kotun cewa matarsa bata bashi hakkinsa na aure, don haka kwanciyar hankali ya kaurace masa

- Sakamakon ganin alamun soyayya tsakanin ma'aurata, mai shari'a ya bukaci su koma gida don sasanci kafin ranar 6 ga watan Augusta

A ranar Juma'a, Abidemi Dada ya roki wata kotun gargajiya da ta tsinke igiyar aurensa mai shekaru 13 da matarsa.

Injiniyan ya tabbatar da cewa matarsa mai sun Opeyemi bata ba shi hakkinsa kuma koyaushe bata aminta da shi.

A yayin sanar da kotun, Dada wanda ke zama a yankin Oke-Bola a Ibadan ya ce: "Kwata-kwata rayuwata ta sauya tunda matata ta fara wasu irin halaye. Tana kaurace min tare da hana ni kusantarta."

"Matata tayi biris da shawarar fastonmu. Babu zaman lafiya a aurenmu. Tana zagina a duk lokacin da ta so," yace

Ya zargi matarsa da daina kula da 'ya'yansu.

Mai shari'a Ademola Odumade ya yi kira ga ma'auratan da su sasanta kansu.

Odumade ya fahimci cewa akwai alamun kauna tsakanin ma'auratan, lamarin da yasa ya yi musu nasiha a kan hakuri.

Ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Augusta don yanke hukunci.

Rayuwata ta sauya tunda matata ta fara hana ni hakkina - Magidanci
Rayuwata ta sauya tunda matata ta fara hana ni hakkina - Magidanci. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: UN ta dakatar da ma'aikatanta 2 a kan bidiyon lalatarsu da ya bazu

A wani labari na daban, Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum mai suba Shuaibu Aliyu sakamakon zarginsa da ake da dirkawa yarinya mai shekaru 14 ciki tare da yadda jaririyar da ta haifa a daji.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani Kaoje ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kama masu laifi. Ya ce an damke wanda ake zargin da laifin fyade da kuma yunkurin kisan kai.

Kaoje ya bayyana cewa, "wani Alhaji Hamisu Abubakar da ke yankin Kalambaina a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto ya kai korafi ofishin 'yan sanda.

"Ya ce wani mutum mai suna Shuaibu Aliyu ya ja yarinya mai shekaru 14 cikin dakinsa inda yayi mata fyade."

Ya kara da cewa, "Sakamakon hakan, ta samu ciki har ta haihu. Ta kai wa wanda ake zargin jinjirin tare da wani abokinsa Nasiru Attahiru wanda yanzu ake name.

"Sun karba tare da jefar da jinjirin a wani daji da ke kauyen Gidan Boka a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel