Gwamna Aminu Masari ya shirya taron addu'a na musamman kan yan bindigan da suka addabi jihar (Hotuna)
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shirya taron addu'a na musamman kan harkokin yan bindigam garkuwa da mutane da satar shanu da ya addabi al'ummar jihar shekarun nan.
A ranar Alhamis, 2 ga Yuli aka kaddamar da wannan taron addu'ar kuma za'a kwashe kwanaki uku ana yi, Channels TV ta samu labari.
An fara na yau ne misalin karfe 10 na safe a Masallacin Juma'ar dake birnin jihar inda mahaddata Al-Kur'ani sama da 300 suke sauka.
An kwashe awanni uku a saukar yau.
A cewar masu ruwa da tsaki, an kaddamar da taron addu'ar ne bisa bukatar al'ummar jihar domin shawo kan lamarin rashin tsaron da ya addabi jihar.
Hakazalika an yi hakan ne domin nunawa jami'an tsaron dake faggen fama cewa al'ummar na nasu iyakan kokarin wajen ganin an kawar da yan binsigan.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sune mataimakin gwamnan jihar, Injiniya MannirYakubu; kwamishanan labarai, Alhaji Abdulkareem sirika; mai baiwa gwamna shawara kan tsaro, Ibrahim Ahmad da sakataren din-din-din ma'aikatar harkokin addini, Mohammad Lawal Mua'zu.
Kalli hotunan:

Asali: Facebook
KU KARANTA: Bayan kamuwar gwamna, Kwamishanan lafiyan jihar Ondo ya mutu sakamakon COVID-19

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng