Yanzu-yanzu: Bayan kamuwar gwamna, Kwamishanan lafiyan jihar Ondo ya mutu sakamakon COVID-19

Yanzu-yanzu: Bayan kamuwar gwamna, Kwamishanan lafiyan jihar Ondo ya mutu sakamakon COVID-19

Innan Lillahi wa inna ilaihi raji'un

Allah ya yiwa Kwamishanan lafiyan jihar Ondo, Dakta wahab Adegbenro, rasuwa.

Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar sun nuna cewa kwamishanan ya rasu ne sakamakon cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Cutar Coronavirus za ta kara dilmiya talakawa cikin matsanancin talauci - Buhari

Yanzu-yanzu: Bayan kamuwar gwamna, Kwamishanan lafiyan jihar Ondo ya mutu sakamakon COVID-19
Kwamishanan lafiyan jihar Ondo ya mutu sakamakon COVID-19
Asali: Depositphotos

Mutuwar kwamishanan ya biyo bayan kamuwar gwamnan jihar da cutar ta Korona.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata 30 ga watan Yuni ta wani faifan bidiyo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Twitter.

Akeredolu ya ce a lokacin da ya samu sakamakon gwajin, baya da alamomin cutar kuma tuni ya killace kansa.

Ya bukaci mutanen jiharsa su taya shi da adduo'i inda ya ce, "a halin yanzu ina bukatar adduoin samun sauki daga gare ku."

A cikin faifan bidiyon, Akeredolu ya ce, "Kwanakin baya na kamu da zazabin cizon sauro kuma na warke. A lokacin da muka tafi taron NEC na jamiyyar mu ta APC, takwarori na sun janyo hankali na.

"Na yi magana da daya daga cikinsu, ya jawo hankali na cewa bai dace a rika wasa da zazzabin cizon sauro ba a halin yanzu na annoba kuma ya ce in tafi in yi gwajin Covid-19.

"Sakamakon gwajin ya fito a ranar 3O ga watan Yunin 22. Sakamakon ya nuna na kamu da cutar. Amma jiki na lafiya kalau ba ni da alamomin cutar. Bana jin wani canji a jiki na. Likitoci na sun ce in fara shan magungunan cutar sannan in killace kai na."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel