Yadda wata mata ta yanke jiki ta fadi mataciyya bayan jin cewa mijinta ya kamu da COVID-19

Yadda wata mata ta yanke jiki ta fadi mataciyya bayan jin cewa mijinta ya kamu da COVID-19

– Watar baiwar Allah ta yanke jiki ta fadi mataciyya bayan samun labarin cewa mijinta ya kamu da korona

– Lamarin ya faru ne a ranar Litinin garin Ughelli da ke karamar hukumar Ughelli na jihar Delta

– Wata majiya ta ce akwai yiwuwar matar tana fama da cutar hawan jini shi yasa ta yanke jiki da fadi mataciya bayan samun labarin

Wata matar aure mai matsakaicin shekaru ta yanke jiki ta fadi a garin Ughelli da ke karamar hukumar Ughelli na jihar Delta bayan samun labarin cewa mijinta ya kamu da cutar coronavirus kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Abin tausayin da ya faru a Igho Salami Street, Uloho Avenue ya jefa makwabta da mutanen garin cikin alhini.

Yadda wata mata ta yanke jiki ta fadi mataciya bayan jin cewa mijinta ya kamu da COVID-19
Yadda wata mata ta yanke jiki ta fadi mataciya bayan jin cewa mijinta ya kamu da COVID-19. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya 12 da suka rasu a watan Yuni

Majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa an hangi mutane sun taru a kusa da gidan marigayiyan suna tattauna lamarin amma ba su son yin magana da baki.

Wata majiya ta ce Mrs Oregbe tana gida a lokacin da labari ya ishe ta cewa sakamakon gwajin da aka yi wa mijinta ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar.

A cewar majiyar, "Ina kyautata zaton tana fama da hawan jini kafin yanzu domin ana fada mata cewa mijin ta ya kamy da cutar coronavirus ta yanke jiki ta fadi kafin a garzaya da ita zuwa asibiti."

A wani labarin daban, Legit.ng ta kawo muku cewa Wole Oyebamiji, sakataren gwamnatin jihar Osun ya kamu da cutar korona.

Kwamishinan lafiya na jihar, Rafiu Isamoto, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata.

Jihar ta tabbatar da harbuwar karin mutum 10 da muguwar cutar bayan sallamar mutum daya da ya warke daga cutar korona.

Kamar yaadda kwamishinan ya bayyana, hauhawar yawan masu cutar a jihar ya biyo bayan halayyar mazauna jihar na take dokokin kariya daga muguwar cutar.

"Idan aka lura, yawan masu cutar ya fara hauhawa ne a makonni biyu da suka gabata. Dalilin kuwa a bayyane yake. Jama'armu na nuna halin ko in kula a kan cutar.

"Rashin kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar na daya daga cikin dalilan da ke kawo yawaitar masu kamuwa. A halin yanzu muna zargin cutar na yaduwa tsakanin mutane," yace.

A cewarsa, "Gwamnati za ta sake duba al'amarin, za mu sanar da dokoki masu tsauri don kiyaye yaduwar cutar.

"A halin yanzu, ko kama mutum aka yi ana tilasta shi killace kansa a matsayin hanyar dakile yaduwar muguwar cutar.

"Za mu kafa kotun tafi da gidanka da za ta fara ladabtar da masu karantsaye ga dokar hana yaduwar cutar. Dole ne mu hada kai da gwamnati wurin hana yaduwar cutar.

"Hakazalika, ina son sanar da ku cewa sakataren gwamnatin jihar da wasu ma'aikatan da ke tattare da shi sun kamu da cutar. Amma da sauki al'amarin don suna samun kulawar da ta dace."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel