Yanzu-yanzu: Wani gwamna da matarsa sun kamu da cutar Korona
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da iyalinsa sun kamu muguwar cutar Coronavirus (COVID19) yan kwanaki bayan kamuwar diyarsu.
Legit Hausa ta samu labari ne daga gwamnan yayinda ya katabta a shafinsa na Tuwita a yau Alhamis, 1 ga watan Yuli, 2020.
Yace: "Ni da iyalina mun kamu da cutar COvID-19. Muna nan cikin koshin lafiya kuma muna cigaba da killace kanmu."
"Muna gode muku gaba daga bisa addu'o'inku akanmu da diyarmu."
Mun kawo muku rahoton cewa Gwamna Ifeanyi Okowa, da maidakinsa, Edith Okowa, sun shiga killace kansu na tsawon kwanaki 14 bayan diyarsu ta kamu da cutar Coronavirus (COVID19) ranar Juma'a, 26 ga Yuni, 2020.
Okowa yace: "A yau din nan, Edith da ni mun samu labarin cewa daya daga cikin 'yayanmu mata ta kamu da cutar COVID19."
"Saboda haka, bisa ga ka'idojin da aka gindaya, zamu shiga killace kanmu na tsawon kwanaki 14."
Gabanin hakan, sakataren gwamnatin jihar, Mista Chiedu Ebere da kwamishanan labaran jihar, Charles aniagwu, sun kamu da cutar Korona karshen makon da ya gabata.
Yanzu haka suna jinya a cibiyar killacewa a jihar, cewar sakataren yada labaran gwamna, Olisa Ifeajika.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng