Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 561 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 561 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 561 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.50 na daren ranar Talata 30 ga Yunin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 561 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 561 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 561 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Asali: Twitter

Lagos-200

Edo-119

Kaduna-52

FCT-52

Niger-32

Ogun-19

Ondo-16

Imo-14

Plateau-11

Abia-8

Oyo-8

Bayelsa-7

Katsina-6

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya 12 da suka rasu a watan Yuni

Kano-5

Bauchi-3

Osun-3

Kebbi-3

Borno-2

Jigawa-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Talata 30 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 25694.

An sallami mutum 9746 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 590.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji matar wani soja, Mrs Victoria Idakpini da mijinta, Lance Corporal Martins Idakpani sun yi karar Rundunar Sojin Najeriya, Shugaban hafsin sojojin kasa da Attoney Janar na kasa saboda take hakkin bil adama.

An kama Mrs Idakpani ne a makon da ta gabata kwanaki kadan bayan kama mijinta, Martins Idakpani, saboda cin mutuncin Shugaban rundunar sojojin kasa, Lt Janar Tukur Buratai, da Shugaban hafsoshin tsaro, Gabriel Olonisakin cikin wani bidiyo da ya rika yawo a intanet.

A cikin bidiyon, sojan ya yi kira ga shugabanin sojojin da su yi murabus tunda sun gaza wurin yaki da ta'addanci.

Ya kuma zarge su da nuna halin ko in kula da a kan batun tsaro a kasar da kuma yadda yan taadda ke cin karensu ba babbaka a kasar.

Ma'auratan cikin wani takardar kara da wani Apeh Abuchi ya shigar a madadinsu, sun ce an hana su ganin lauya kuma ba a sanar da su laifin da suka aikata ba tun kama su a makon da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Akinyodem wanda shine shugaba na kasa na kungiyar lauyoyi ta Revolutionary Lawyers’ Forum, ya bayyana cigaba da tsare ma'auratan a matsayin saba doka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel