Mun fasa zuwa kotu - Tsaffin shugabannin APC da aka kora

Mun fasa zuwa kotu - Tsaffin shugabannin APC da aka kora

Da alamun zaman lafiya ya dawo jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga karshe yayinda yan kwamitin majalisar gudanarwar da aka rusa ranar Alhamis sun fasa zuwa kotu, The Nation ta ruwaito.

Tsohon Sakataran kwamitin shugabannin jam'iyyar, Malam Waziri Bulama, ya bayyana haka jiya inda yace sun yanke shawara kawai a zauna lafiya.

Ya ce zaben 2023 ne ya sabbaba rikicin jam'iyyar yanzu.

Mun fasa zuwa kotu - Tsaffin shugabannin APC da aka kora
Mun fasa zuwa kotu - Tsaffin shugabannin APC da aka kora
Asali: Twitter

KU KARANTA: An cire hotunan Adams Oshiomole daga sakatariyar APC

Bulama yace: "Bayan mun nemi shawari daga wajen manya da masu ruwa da tsaki, mun amince da shawarar rusa kwamitin NWC da kuma kafa sabuwar kwamitin rikon kwarya karkashin Gwamna Mai Mala Buni."

"Muna ganin girman shugaban kasa. Mu ba yan tawaye bane. Duk maganganun da mukayi na cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar."

"Yanzu mun ajiye duk wata maganar kundin mulki ko kotu saboda zaman lafiya ya wanzu cikin jam'iyyar. Muna ganin girman manya, mun kira ga masu ruwa da tsaki kada su sake tayar da hayaniya cikin jam'iyyar."

"Zamu baiwa kwamitin Buni hadin kai wajen shirya taron gangami cikin watani shida masu zuwa."

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cew shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar All Progressives Congress APC da wasu gwamnoni a fadar Aso Villa yau Juma'a, 26 ga Yuni, 2020.

Gwamnonin wanda shahararrun masu adawa da tsohon shugaban APC Adams Oshiomole sun kai ziyarar domin yi ma Buhari godiya kan yadda ya shawo kan rikicin da ya kusa warware tsintsiyar jam'iyyar.

Daga cikin gwamnonin da suka kai ziyarar akwai gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya, Mai Mala Buni; da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Sauran sune gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel