'Yan bindiga sun sace diyar dakaci a Katsina

'Yan bindiga sun sace diyar dakaci a Katsina

'Yan bindiga a yammacin ranar Talata sun kai hari kauyen Karare da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina inda suka sace diyar dagajin kauyen, Ciroma Ahmadu Karare.

Mazauna kauyen sun ce 'yan bindigan sun sace matashiyar mai shekaru 20 tare da wata mata mai shekara 23 da ke da goyo a bayanta a lokaci da aka yi awon gaba da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yan bindigan da aka ce adadinsu ya kai 20 sun isa kauyen ne a kan babura dauke da bindigu kamar yadda suka saba.

Katsina: 'Yan bindiga sun sace diyar dagajin Karare
Katsina: 'Yan bindiga sun sace diyar dagajin kauye. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sarki a Najeriya ya shiga jerin manyan sarakuna 5 a nahiyar Afrika

Rahotanni sun ce sun bi gidaje da dama suna yi wa mutane fashi ciki har da gidan dagajin kauyen inda suka sace diyarsa.

Daya daga cikin mazauna kauyen, Mustapha Ruma ya ce yan bindigan sun kwace wayar dagajin kauyen sannan suka ba shi sabon layin waya.

Sun umurci ya kira su domin tattauna abinda zai biya domin fansar diyarsa.

Yan bindigan kuma sun sace wasu dabobi da kayan abinci daga wurin mazauna kauyen yayin harin.

Da aka tuntube shi a wayar tarho, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce "har yanzu ina bincike a kan lamarin".

Bai kira ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.

Mashawarcin gwamna Aminu Masari na musamman a kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina shima bai amsa sakon ko kirar waya da aka masa ba don ji ta bakinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel