Matar aure ta bai wa mijinta kyautar akwatin gawa a ranar 'Father's Day'

Matar aure ta bai wa mijinta kyautar akwatin gawa a ranar 'Father's Day'

A yayin da matan aure ke jinjinawa mazansu na aure a ranar mahaifa na duniya, wata mata a Anambra ta fita zarra.

Ta bai wa jama'a da dama mamaki bayan da ta siya akwatin gawa ta bai wa mijinta a matsayin kyauta, jaridar Within Nigerian ta wallafa.

Matar na zama ne a Oko, karamar hukumar Orumba ta arewa ta jihar Anambra. Ta mika kyautar akwatin gawa ga mijinta a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni.

Kamar yadda rahoto ya bayyana, matar ta siyo akwatin gawa kwanaki hudu kafin ranar, ta ajiye tana jiran ranar mahaifan ta duniya.

Bayan kammala bauta a ranar Lahadi, ta garzaya wurin mai siyar da akwatin sannan ta sa aka kai mata shi gida sannan ta mika ga mijinta.

"Mun sha mamaki da ta shigo gida da akwatin gawa. Babu wanda ya fahimceta," wata majiya daga iyalansa ta tabbatar.

Matar aure ta bai wa mijinta kyautar akwatin gawa a ranar 'Father's Day'
Matar aure ta bai wa mijinta kyautar akwatin gawa a ranar 'Father's Day'. Hoto daga Within Nigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba

A wani labari na daban, wani mutum dan Najeriya me zama a Victory Park Estate da ke Lekki a jihar Legas, ya kashe kansa bayan ya sokawa matarsa wuka har lahira.

Bala Elkana, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga The Cable Lifestyle a ranar Litinin, ya ce an adana gawawwakin mamatan a ranar Lahadi.

Ya ce a lokacin da 'yan sandan suka isa wurin da abun ya faru, kumfa ce ke fita daga bakin mutumin, lamarin da ke nuna cewa guba ya sha.

Matarsa kuwa na kwance a cikin jininta. Elkana ya ce an dauke wukar wacce ake tunanin an yi amfani da ita wurin kashe matar tare da kwalaben Sniper, wanda ake tsammanin ya yi amfani da shi wurin kashe kansa.

Kakakin ya kara da cewa, yayin da ake binciken yadda lamarin ya auku, ana tsammanin mutumin ya soka wa matarsa wuka sannan ya kashe kansa daga baya.

"Zan iya tabbatar muku da aukuwar lamarin. Mun mika gawawwakin asibiti don gwajin abinda ya kasheta. Mun ganta a cikin jini," Elkana ya sanar da The Cable Lifestyle.

"Wukar yanka ce aka samu a wurin tare da kwalbar sniper biyu wacce ake tsammanin ya sha domin kumfa ce ke fita daga bakinsa.

"Likitoci za su gano silar mutuwarsu duk da hasashe a yanzu na nuna cewa ya kasheta ne sannan ya kashe kansa. Ana ci gaba da bincike," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel