Hajj 2020: Sharruda 6 da Saudiyya ta gindaya kan Hajjin bana

Hajj 2020: Sharruda 6 da Saudiyya ta gindaya kan Hajjin bana

Gwamnatin kasar Saudiyya ta lissafa sharruda shida dukkan masu niyyar zuwa sauke farali a kasar mai tsarki a shekarar 2020 za su cika don yin aikin Hajjin na bana.

Mahukunta a kasar ta Saudiyya a baya sun bayyana cewa mazauna kasar ta Saudiyya ne kawai za a bawa daman yin aikin hajjin a bana saboda annobar coronavirus.

A yayin taron manema labarai a ranar Talata, Ministan Lafiya na Saudiyya, Tawfiq Al-Rabiah ya ce za a bawa wadanda shekarunsu bai haura 65 ba kuma masu cikaken lafiya daman zuwa sauke faralin.

Ya kara da cewa kuma za a yi wa maniyyatan gwajin coronavirus kafin a bari su shiga kasa mai tsarkin kuma za su kwashe kwanaki 14 a killace a masaukinsu bayan kammala aikin hajjin.

Hajjin 2020: Saudiyya ta lissafa sharruda shida na yin aikin Hajjin bana
Hajjin 2020: Saudiyya ta lissafa sharruda shida na yin aikin Hajjin bana. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Ministan lafiyar ya kuma bayyana cewa an tanadi matakai don ganin maniyyatan sunyi aikin hajjin a yanayin bayar da tazara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce za a kayyade adadin maniyyatan da za suyi aikin hajjin kuma akwai yiwuwar ba za su wuce 10,000 ba.

"An tanadi asibitoci a wurare da dama saboda yiwuwar samun wadanda ke bukatar taimakon gaggawa baya ga cibiyar lafiya da ke Dutsen Arafat," in ji shi.

"Likitoci da motoccin asibiti za su rika yawo tare da maniyyatan a yayin da suka ibadojinsu.

"Munyi shiri na musamman domin aikin Hajjin bana.

"Za ayi aikin Hajjin cikin lafiya a kare lafiya," in ji shi.

Ga sharrudan shida da ministan lafiyar na Saudiyya ya lissafa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun damke 'yan KAROTA uku a Kano

1. Wadanda shekarunsu ya haura 65 ba za su tafi aikin Hajji ba

2. Mutane masu cututtuka kamar ciwon sukari, hawan jini da sauransu ba za su tafi hajji ba

3. Za a yi wa kowane maniyyaci gwajin coronavirus kafin zuwa Hajji

4. Za a rika bayar da tazara yayin aikin Hajji

5. Za a rika duba lafiyar maniyyata a kowane rana

6. Za a killace maniyyata na kwanaki 14 bayan kammala aikin Hajji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel