Magidanci ya kashe 'ya'yansa biyu da tabarya, ya raunata mahaifinsa

Magidanci ya kashe 'ya'yansa biyu da tabarya, ya raunata mahaifinsa

Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da kama wani mutum mai shekaru 34 mai suna Ifeanyi Apusiobi da ke Azu Ogbunike a karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra a kan zarginsa da ake da kashe 'ya'yansa biyu da tabarya.

Wanda ake zargin ya rafke 'ya'yansa biyu; Chinecherem Apusiobi mai shekaru 7 da Obinna Apusiobi mai shekaru 5 da tabarya yayin da suke bacci tare da raunata mahaifinsa mai shekaru 72 mai suna Dominic Apusiobi.

Tuni sashen bincike na musamman na 'yan sandan jihar suka samu shaidu don fara bincike, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kamar yadda takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya fitar, ta ce "A ranar 21 ga watan Yunin 2020 wurin karfe 1 na dare, jami'ai daga ofishin 'yan sanda da ke Ogbunike sun damke wani mutum mai suna Ifeanyi Apusiobi mai shekaru 34 a Azu Ogbunike da ke karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra.

"Wanda ake zargin ya hari 'ya'yansa biyu inda ya kashesu har lahira da tabarya. Ya raunata mahaifinsa mai shekaru 72 a kai."

A halin yanzu, jami'an yan sanda sun ziyarci inda al'amarin ya faru tare da mika yaran biyu asibiti inda aka tabbatar da mutuwar su. Amma mahaifinsa na samun sauki.

An adana gawawwakin a ma'adanar gawa da ke asibitin Isienyi.

Magidanci ya kashe 'ya'yansa biyu da tabarya, ya raunata mahaifinsa
Magidanci ya kashe 'ya'yansa biyu da tabarya, ya raunata mahaifinsa. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara (Hotuna)

A wani labari na daban, a kalla mutum bakwai suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai kauyukan Kasai da Nahuta da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Jaridar HumAngke ta gano cewa, mutum shida ne ruwa ya ci wanda ya hada da mace mai juna biyu a yayin da suka yi yunkurin tserewa daga kauyen sakamakon harin.

Ganau ba jiyau ba, sun ce 'yan bindigar sun kashe mutum daya a harin yayin da ake neman mutane biyu wadanda ake zargin sun bace duk da 'yan bindigar sun kwashe musu kadarori.

An gano cewa kauyawan sun arce zuwa daji don gujewa harin yayin da 'yan bindigar suka dinga harbin duk abinda suka yi ido biyu da shi.

Mustapha Ruma, wanda ya tsallake harin, ya ce 'yan bindigar sun tsinkayi kauyukansu ne a babura rike da miyagun makamai a yayin da jama'a ke sallar jam'i.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel