Dirama ta koma Ondo: Gwamna ya sa 'yan sanda sun damke mataimaki ana gobe zai koma PDP (Bidiyo)

Dirama ta koma Ondo: Gwamna ya sa 'yan sanda sun damke mataimaki ana gobe zai koma PDP (Bidiyo)

An yi gajeruwar dirama a jihar Ondo daren Asabar yayinda kwamishanan yan sandan jihar, Bolaji Salami, ya hana mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, fita daga cikin gidan gwamnati.

Kwamishanan ya dakatad da mataimakin gwamnan ne tare da wasu hadimansa yayinda suke kwashe kayansu daga gidan gwamnatin bisa umurnin gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

A bidiyon da TheCable ta samu, ya nuna sai da suka kwashe sa'o'i suna mujadala amma yan sanda basu bari ya fita ba.

Gwamna Akeredolu da mataimakinsa sun dade da shiga takun tsaka kuma rahotanni sun bayyana cewa mataimakin ya yanke shawarar sauya sheka jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin fito na fito da gwamnan a zabe.

Dirama ta koma Ondo: Gwamna ya sa 'yan sanda sun damke mataimaki don zai koma PDP (Bidiyo)
Akeredolu
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An dawo da Adams Oshiomole

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Allen Sowore, ya bayyanawa manema labarai cewa an tsare maigidansa na tsawon sa'o;i da dama, duk da cewa doka ta bashi kariya.

Yace: "Mun kasa fita daga gidan gwamnati na tsawon awanni jiya saboda sun haka mataimakin gwamnan kwashe kayansa."

Amma hadimin gwamnan kan sabbin kafafen labarai, Richard Olatunde, ya ce an hana mataimakin gwamnan fita ne saboda yana kokarin kwashe wasu dukiyoyin gwamnati.

"An kama Hadiman mataimakin gwamnan jiya da wasu dukiyoyin gwamnati. Wasu daga cikinsu sun kwashe dukkan kayan daki da sunan cewa shi ya gyara."

"Sun dauke Talabijin, da ikirarin cewa mataimakin gwamnan ya saya sai kace ofishin mataimakin gwamna ba mallakin gwamnati bane."

"Saboda haka masu gadi suka tilasta musu mayar da kayayyakin, kuma maimakon suyi haka sai suka kira mataimakin gwamnan, shi kuma ya zo da su daga baya." A cewarsa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel