Kudin da ake kashewa jami'an gwamnati ya yi yawa, ya kamata a sake dubawa - Osinbajo

Kudin da ake kashewa jami'an gwamnati ya yi yawa, ya kamata a sake dubawa - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa ya kamata a sake zama a tattauna irin kudaden da ake bannatarwa akan manyan jami'an gwamnati a kasar nan.

Ya ce abin na da wuya saboda wadanda zasu yi gyaran na amfana da yanayin; amma dai wajibi ne a san na yi.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyin tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, a taron yanar gizon da Cocin Emmanuel ta shirya kan tattalin arzikin Najeriya idan COVID-19 ta gushe.

Sanusi yace: "Jihar Atalanta (a Amurka) na da GDP wanda ya fi na Najeriya, kuma fa ba Atlanta bace jiha mafi arziki a Amurka."

"Cinikin da kamfanin Tesla ke yi a shekara ya fi kasafin kudin Najeriya, shin ba ka tunanin ya kamata mu rage yadda muke bannatar da kudi; shin bai kamata mu sake duba wannan kundin tsarin mulkin ba da kanta."

"Misali a mayar da aikin majalisa wucin gadi, a mayar da Majalisa daya maimakon biyu, a mayar da kananan hukumomi karkashin wata ma'aikata daban?"

A martaninsa, Osinbajo yace: "Ko shakka babu muna wani irin gwamnati mai tsada, amma kamar yadda ka sani, dubi ga wannan kudin tsarin mulkin, wadanda ya kamata su rage abin, musamman, a mayar yan wucin gadi sune yan majalisa."

"Saboda haka zai yi wuya a samu wani nasara idan aka bukacesu su canza abinda suke matukar amfana da shi."

"Saboda haka akwai bukatar kasar nan ta sake zama na musamman akan lamarin nan kuma ya kamata mu tabbatar da cewa bamu bannatar da dukiyar da ya kamata a ciyar da kasa gaba da shi wajen biyan alawus."

"A yanzu kashi 70% na kudin shiganmu alawus ake biya da su , saboda haka ko shakka babu ya kamata a rage."

Kudin da ake kashewa jami'an gwamnati ya yi yawa, ya kamata a sake dubawa - Osinbajo
Osinbajo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan kwanaki 90, Za'a bude Masallatan birnin Makkah gobe

Idan baki manta ba a ranar Juma'ar da ta gabata, tsohon sarkin Kano ya bayyana cewa idan ba'a canza yadda ake gudanar da gwamnati a Najeriya ba, kasar za ta talauce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel