Ministan Sharia, Malami, ya aikewa Buhari wasika, ya bukaci a cire Ibrahim Magu

Ministan Sharia, Malami, ya aikewa Buhari wasika, ya bukaci a cire Ibrahim Magu

Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami SAN, ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari wasikar kar ta kwana kan shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

Malami ya bukaci shugaban kasan ya tsige shugaban hukumar hana almundahanan bisa wasu zarge-zargen rashawa akalla 20.

A cewar rahoton Thisday, daga cikin zarge-zargen da Abubakar Malami ya yiwa Ibrahim Magu shine yana karkatar da kudaden sata kuma bashi da biyayya ga na gaba dashi a gwamnati.

Thisday ta samu labari daga majiyoyi daban jiya cewa Malami ya bada jerin sunayen mutane uku da Buhari kan maye Ibrahim Magu dasu.

Amma magoya bayan Magu dake cikin fadar shugaban kasa na cewa "cire Magu a wannan lokaci da yake kokari tukuru na yaki da rashawa a gwamnatin Buhari na iya zama babban kuskure.

Majiyoyin suka ce: "Abin takaici ne shugaban EFCC na fuskantar wasu miyagu da suka rantse sai sun cireshi duk da nasarorin da ya samu."

Amma fa sunce dubi ga irin tuhume-tuhumen da ake yiwa Magu, da yiwuwan shugaban kasa zai bukaci nada kwamitin bincike kafin yanke shawara.

Ministan Sharia, Malami, ya aikewa Buhari wasika, ya bukaci a cire Ibrahim Magu
Ibrahim Magu
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara

Daya daga cikin majiyoyin yace: "Ina mai tabbatar muku cewa duk da cewa Magu ya tsallake ramukan muguntan da aka shirya masa a baya, na antoni janar din nan mafi karfin da ka iya tuge Magu daga EFCC saboda wasikar AGF na kunshe da tuhume-tuhume 22 masu nauyi da zai wajabtawa Buhari aika sunansa majalisa ko canzashi."

Dalilin da ya sa hakan shine ma'aikatar Antoni Janar ke kula da hukumar EFCC saboda haka ba za'ayi watsi da shawararsa ba."

Wasu majiyan suka ce: "Malami na tuhumar Magu da girman kai da rashin biyayya gareshi a matsayin Minista mai kula da ma'aikatar EFCC."

Malami ya yi ikirain cewa Magu ya sayar da yawancin dukiyoyin da EFCC ta kwato ba tare da sanin kowa ba, majiyan suka kara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel