Yanzu-yanzu: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara

Yanzu-yanzu: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara

Shugaban Alkalan Najeriya, Alkali Tanko Muhammad ya rantsar da Monica Dongban-Mensem matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara a yau Juma’a, 19 ga watan Yuni, 2020.

Hotuna daga tashar TVC sun nuna yadda wadanda suke hallare a bikin ranstarwan suke baiwa juna tazara biyayya ga sharrudan hukumar hana yaduwar cututtuka watau NCDC.

A ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni ne majalisar dattijai ta amince tare da tabbatar da nadin Monica Dongban - Mensem a matsayin shugabar kotun daukaka kara na Najeriya.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana shirin bangaren yin doka na bawa kokarin gyaran bangaren shari'a duk wata gudunmawa da ta dace.

Tabbatar da Dangban - Mensem ya biyo bayan la'akari da rahoton kwamitin majalisar dattijai a kan bangaren shari'a da kare hakkin bil adama wanda Sanata Opeyemi Bamidele (Ekiti ta tsakiya) ke jagoranta.

KU KARANTA: WHO ta ayyana Najeriya ta yi sallama da cutar shan inna

A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar dattawa, sunan Jastis Monica Dongban-Mensem, a matsayin sabuwar shugaba ta kotun daukaka kara domin tantancewa da tabbatarwa.

Bisa ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa shugaba Buhari, yana neman amincewar majalisar wajen nadin Jastis Monica, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, shi ne ya wallafa sanarwar hakan a kan shafinsa na Twitter a Litinin, 8 ga watan Yunin 2020.

Haka kuma shugaban kasar ya tabbatar da wannan sanarwa da kansa a sakon da aka wallafa kan shafinsa na dandalin sada zumunta da Yammacin ranar Litinin.

Yanzu-yanzu: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara
Yanzu-yanzu: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara
Asali: Twitter

Yanzu-yanzu: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara
Yanzu-yanzu: Shugaban Alkalai ya rantsar da sabuwar shugabar kotun daukaka kara
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel