Ba zamu koma bakin aiki ba, sai dai a sallamemu - Likitoci masu yajin aiki sun mayarwa gwamnati martani

Ba zamu koma bakin aiki ba, sai dai a sallamemu - Likitoci masu yajin aiki sun mayarwa gwamnati martani

Kungiyar Likitocin Najeriya ta siffanta barazanar gwamnatin tarayya na sallamarsu daga aiki ko kin biyansu albashi idan basu koma bakin aiki ba a matsayin wasan yara.

Shugaban kungiyar, Aliyu Sokomba, ya bayyana cewa "barkwanci kawai gwamnati keyi" kuma ko kadan hakan ba zai baiwa Likitoci tsoro ba.

Hakazalika ya lashi takobin cewa za su cigaba da yajin aikinsu har sai an biyasu dukkan bukatunsu.

Ba zamu koma bakin aiki ba, sai dai a sallamemu - Likitoci masu yajin aiki sun mayarwa gwamnati martani
Likitoci masu yajin aiki sun mayarwa gwamnati martani
Asali: Depositphotos

KU KARANTA WANNAN: Shuggaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta yi barazanar sallamar likitocinta daga aiki muddin ba su yi watsi da maganar zuwa yajin-aiki, su ka koma asibitoci domin su cigaba da kula da marasa lafiya ba.

Gwamnatin Najeriya ta umurci likitocin su koma aiki a ranar Laraba, inda ta ce za ayi bincike kuma a hukunta duk wanda aka samu bai hallara a asibiti ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnati ta bukaci shugabannin asibitoci su rika ajiye littafin da za a rika sa hannu a duk lokacin da aka shiga ofis domin a tabbatar da masu zuwa aiki.

Wannan barazana ta fito ne daga bakin ministan harkar lafiya na kasa, Osagie Ehanire, bayan an gaza samun matsaya a zaman tattaunawar da su ka yi da kungiyar manyan likitocin.

Kungiyar NARD likitoci mataki na biyu a Najeriya sun shiga yajin aiki ne a ranar Litinin. Har yanzu dai ministan harkar kiwon lafiyan ya gaza shawo kan likitocin kasar.

A zaman da aka yi ranar Talata wanda aka fara da kimanin karfe 1:00, an tashi baram-baram babu matsaya tsakanin bangarorin inda shugaban NARD, Aliyu Socumba, ya fice a fusace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel