Yanzu-yanzu: Zan shirya taron majalisar zartarwa na ba da dadewa - Sabon shugaban APC ya yi tsokaci

Yanzu-yanzu: Zan shirya taron majalisar zartarwa na ba da dadewa - Sabon shugaban APC ya yi tsokaci

- Sanata Abiola Ajimobi ya yi tsokaci kan nada shi mukaddashin shugaban uwar jam'iyyar APC

- Tsohon gwamnan jihar Oyon ya ce nan ba da dadewa ba zai shirya zaman majalisar zartarwan jam'iyyar

- Akwai rahotannin da cewa Sirikin Gandujen na kwance a asibiti bayan kamuwa da COVID-19

Sirikin Ganduje, Sanata Abiola Ajimobi ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai gudanar da zaman majalisar zartarwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) don shawo kan lamura.

Tsohon gwamnan na jihar Oyo ya bayyana hakan ne yayinda yake tsokaci kan nadashi mukaddashin shugaban jam'iyyar ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020.

Gabanin nadashi, Ajimobi ya kasance mataimakin shugaban mai wakiltar yankin kudancin Najeriya.

Ajimobi ya yi kira da masu ruwa da tsaki su kwantar da hankulansu kafin ya shiga ofis domin warwarewar lamuran.

Ajimobi ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji inda yace: " Saboda haka mu kasance cikin zaman lafiya tsakaninmu har sai mun shirya taron NEC domin yanke shawara kan yadda za'ayi."

Yanzu-yanzu: Zan shirya taron majalisar zartarwa na ba da dadewa - Sabon shugaban APC ya yi tsokaci
Governor Ajimobi
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 13, sun ceto mata da yara 32 (Hotuna)

Wannan ya biyo bayan jawabin mataimakin sakataren APC, Victor Giadom inda ya fito ya na sukar wannan matsaya da jam’iyyarsa ta dauka inda ya nuna cewa shi ne ya dace ya dare kan kujerar shugaban jam’iyyar.

Magoya bayan Cif Victor Giadom a tafiyar jam’iyyar APC sun fara nuna adawarsu ga Abiola Ajimobi. Wadanda ke tare da Giadom sun bayyana haka ne a wani jawabi da su ka fitar a jiya.

Legit Hausa ta kawo muku rahoto a daren Talata cewa Uwar jam’iyyar All Progressives Congress APC ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Ajibola Ajimobi, matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar.

Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da dakatad da Adams Oshiomole matsayin shugaban jam’iyyar.

Kakakin jam'yyar ta APC, Mallam Lanre Issa-Onilu ya bayyana hakan a shafin jam’iyyar na Tuwita.

Yace: "Bisa da ofishin lamuran dokanmu da kuma sashe 14,2 (iii) na kundin tsarin mulkin jam'iyyar, mataimakin shugaban jam'iyyar (Kudu), Sanata Abiola Ajimobi zai zama mukaddashin shugaban jam'iyya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel