Harbi a Aso Rock: An sauyawa masu tsaron Aisha Buhari wurin aiki

Harbi a Aso Rock: An sauyawa masu tsaron Aisha Buhari wurin aiki

Dukkan jami'an tsaron da ke da hannu a harbin da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja an sako su kuma an sauya musu wurin aiki.

Majiya mai karfi ta sanar da Daily Trust a daren jiya cewa, wadanda aka sauya wa wurin aikin duk hadiman Aisha Buhari ne har da ADC dinta, Usman Shugaba tare da kwamandan dogaranta.

A daya bangaren kuwa, mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Sabiu Tunde Yusuf, ya koma bakin aikinsa inda yayi watsi da bukatar killace kansa bayan dawowa daga Legas.

Sabiu, wanda aka fi sani da Tunde, sunan da ya samu daga Tunde Idiagbon, an ganshi a fadar shugaban kasar da ke Abuja a jiya.

Idan za mu tuna, Aisha Buhari ta tunkari Tunde da bukatar ya killace kansa don mutunta dokokon dakile yaduwar cutar korona.

Arangamar uwargidan shugaban kasa da Tunde tare da 'ya'yanta ta tada kura a fadar shugaban kasar. Lamarin da yasa masu tsaron lafiyarta suka yi harbi, karantsaye ga dokar fadar shugaban kasar.

Wannan ci gaban ya kawo damke dogaran matar shugaban kasar wanda ya hada da ADC Shugaba da kwamandan dogaranta.

Fusatar da Aisha Buhari tayi yasa ta je shafinta na twitter inda ta bukaci shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu da ya gaggauta sakin hadimanta.

Daily Trust ta gano cewa shugaban kasa Buhari bai damu da wannan ci gaban ba duk da Tunde bai killace kansa ba.

Harbi a Aso Rock: An sauyawa masu tsaron Aisha Buhari wurin aiki
Harbi a Aso Rock: An sauyawa masu tsaron Aisha Buhari wurin aiki. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotu ta jaddada dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban APC

Aliyu Abdullahi, kakakin uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce uwar dakinsa ta daina magana a kan al'amarin da ya faru tsakaninta da Sabiu Yusuf saboda sun juya manufarta.

Abdullahi, wanda ya zanta da gidan talabijin din Channels a ranar Lahadi, ya ce har a halin yanzu hadimanta da aka garkame suna tsare ba a sako su ba.

Uwargidan shugaban kasar cikin kwanakin nan ta yi wa sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, kiran gaggawa a kan sakin hadimanta da ya tsare.

A yayin da aka tambayi hadimin uwargidan shugaban kasar ko suna nan tsare har yanzu, ya ce, "har a halin yanzu suna hannun 'yan sanda. Na san shugaban jami'an tsaron, kwamandan masu mata rakiya da 'yan sandan ofishinta duk suna tsare.

"Tana yin magana a gaban kowa amma ta daina magana ne saboda mutane basu fahimtarta kuma suna juya maganarta.

"Amma gaskiya a koda yaushe tana yin fatan alheri ga kasar nan ta yadda daga ita har 'ya'yanta za su samu natsuwa ko bayan sun sauka mulki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel