Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 490 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 17,148

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 490 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 17,148

Hukumar hana yaduwar Cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da cewa annobar cutar Korona ta sake harbin sabbin mutane 490 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 12:00 na daren ranar Talata, 16 ga watan Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 490 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-142

FCT-60

Bayelsa-54

Rivers-39

Delta-37

Oyo-30

Kaduna-26

Imo-23

Enugu-19

Kwara-17

Gombe-11

Ondo-10

Bauchi-8

Ogun-7

Borno-6

Benue-1

Jimillan wadanda suka kamu - 17,148

Jimillan wadanda suka warke - 5,623

Jimillan wadanda suka mutu - 455

KU KARANTA: Uwar Jamiyyar APC ta nada Sanata Ajimobi matsayin sabon shugaba

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel