'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 25 a Zamfara

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 25 a Zamfara

Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne a ranar Litinin sun sace a kalla mutum 25 a jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a garin Bindin da ke karamar hukumar Maru na jihar Zamfara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindigan da suka kai farmakin sun yi wa garin kawanya ne sannan suka aike da kimanin mutum shida daga cikinsu zuwa cikin garin don aiwatar da abinda suka zo yi.

"Gida gida suke shiga suna zaban mutane. Sun tafi da mutanen cikin daji sun ce iyalansu su biya kudin fansa kafin a sako su.

"Daya daga cikin wadanda suka sace ya yi saa ya tsere sannan sun sako wata mata saboda tana da jariri," inji wani mazaunin garin.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 25 a Zamfara
'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 25 a Zamfara. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Da yardarsu muke saduwa', inji magidancin da ke zina da 'ya'yansa mata biyu

An yi kokarin ji ta bakin Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar, SP Muhammad yayin rubuta wannan rahoton amma hakan ya ci tura.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa Gwamnan Katsina, Aminu Masari ya ce ya gaza sauke nauyin da ke kansa na kare Katsinawa daga sharrin 'yan bindiga.

Da ya ke hira da manema labarai a gidan gwamnati a Katsina, Masari ya ce yana bakin ciki saboda tun hawarsa mulki Katsinawa ba su runtsa ba.

Ya ce gara dabobi da yan bindigan domin su kashe mutane barkatai suke yi babu dalili kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ban san abinda zan fada musu ba. Ba zan iya kallon kwayoyin idanunsu ba domin mun gaza kare su akasin alkawarin da muka dauka na kare rayuka da dukiyoyinsu a jihar," in ji gwamnan.

"Ban taba tsamanin yan bindigan da ke zaune a daji za su aikata haka ba, halin da suke nuna wa yafi na dabobi muni.

"A daji, zaki ko damisa kan kashe dabba ne kawai idan yana jin yunwa kuma ba dukka dabobi ya ke kashe wa ba, wanda zai ci kawai ya ke kashe wa a lokaci guda.

"Amma abinda muke gani shine yan bindiga za su shigo gari, suyi ta ruwa harsashi suna kashe mutane ba dalili, kamar kisar da aka yi baya bayan nan a Faskari da wasu sassan karamar hukumar Dandume.

"Ta yaya mutum zai rika aikata abinda ko dabba ba zai aikata ba?”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel