Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)

Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)

Wata mata mai shekara 65 mai suna Mbah Gambreng da danta na riko, Ardi Waras sun yi aure a kudancin Sumatra da ke kasar Indonesia kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Rahotanni sun ce Gambreng dan ta na riko, yanzu mijinta Ardi ya kwashe kimanin shekara guda yana zaune tare da ita tun bayan daura auren duk da cewa ta yi ikirarin cewa ba ta da niyyar aurensa a wannan lokacin.

Ta ce ta yi matukar mamaki a lokacin da ya nemi ta aure shi.

An daura auren masoyan biyu a gaban 'ya'yan ta na riko mata guda uku.

An ruwaito cewa ta ce – “Na yi mamaki sosai yadda ya nemi in aure shi.”

An ce Ardi ya biya Rupiah 100,000 a matsayin sadaki kamar yadda ango ko mahaifinsa ke biyan sadaki ga amarya kafin daura aure.

Ga hotunan auren a kasa;

Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)
Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)
Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Da yardarsu muke saduwa', inji magidancin da ke zina da 'ya'yansa mata biyu

Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna)
Tsohuwa mai shekara 65 ta auri ɗanta na riƙo mai shekara 24 (Hotuna). Hoto daga The Nation
Asali: UGC

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, jami'an 'yan sanda a jihar Niger sun kama wasu maza biyu, a babban birnin jihar MInna dauke da katin cire kudi a na'urar ATM guda 36.

'Yan sandan sun ce wadanda ake zargin suna damfarar mutane da suka zo cire kudade a naurar ta ATM ne da sunan taimaka musu.

Victor Okebugwu mai shekaru 32 da James Amaonye mai shekaru 33 sun shafe fiye da shekaru biyu suna damfarar ta ATM kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Amaonye ya ce sun fara damfarar ne a babban rukunin kantina da ke Minna, Obasanjo Complex daga nan kuma suka fara zuwa bankuna.

Ya ce, "Idan mun ga mutanen da suke bukatar taimako a gaban na'urar ATM, mu kan matsa kusa da su da sunan taimako. Mafi yawancin lokaci suna bari mu taimaka musu.

"Mu kan sauya katinsu da jabu wasu lokutan kuma mu kan aika kudade daga asusun ajiyar su zuwa namu ba tare da sun sani ba. Mun dade muna wannan harka."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da kama wadanda ake zargin inda ya ce 'yan sandan sun dade suna lura da su.

Abiodun ya ce katin na ATM 36 na bankuna daban–daban ne, an kuma gano layin waya, sim card, guda 24 a hannun su.

Abiodun ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel