Sarakunan gargajiya a Katsina na da hannu cikin hare-haren da ake kaiwa al'ummarsu - Fadar shugaban kasa

Sarakunan gargajiya a Katsina na da hannu cikin hare-haren da ake kaiwa al'ummarsu - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa akwai sarakunan gargajiya a jihar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake daukan nauyin yan bindigan dake kashe al'ummarsu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hirar da yayi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV.

Ya bayyana cewa wannan dalilin ya sa aka samu yawan hare-hare da kashe-kashe a jihar.

Yace: "Ba wai muna zargin wani da laifi bane amma maganan gaskiya shine ko a mahaifar shugaban kasa, akwai wasu sarakunan gargajiya da aka kama da hannu cikin hada baki da yan bindiga wajen cutar da al'ummarsu."

"A jihar Zamfara, an kwancewa sarakuna da dakatai rawaninsu. Gaskiyar magana itace akwai masu amfana daga kowani lamarin lalaci."

KU KARANTA: Badakala: Ana zargin John Ohireime Asein da aika-aika a NCC

Sarakunan gargajiya a Katsina na da hannu cikin hare-haren da ake kaiwa al'ummarsu - Fadar shugaban kasa
Hakkin Mallaka: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Shehu ya kara da cewa yayinda rikicin yan ta'adda ya yi tsamari a jihar Zamfara, dakarun Sojin sama sun kafa tashar jirgin sama a Katsina yadda zasu iya far wa yan ta'adda a Zamfara ko da yaushe.

Amma jirgin na tashi, wasu marasa kishi a Katsina zasu tuntubi yan ta'addan dake Zamfara cewa ga shi Sojoji zasu kai hari saboda haka su gudu.

A cewar Garba Shehu: "A wasu lokutan da suka gabata, hukumar mayakan sama ta ajiye wasu jirage a Katsina, har yanzu suna waje."

"Sun gano cewa jirgin yaki na tashi daga tashar jirgin saman Katsina, kafin ta isa Zamfara domin ragargazansu, an kirasu a waya cewa ga Sojoji nan zuwa, sai su gudu."

"Daga karshe hakan ya tilasta mana tashi daga wurare masu nisa irinsu Kaduna da Kano domin kai hari Zamfara."

Jihar Katsina a kwanakin bayan nan na fusktantar barazanan yan bindiga inda aka hallaka rayukan mutane da dama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel