Maryam Abacha ta yi magana a kan karairayin da ake yadawa a kan tsohon mijinta

Maryam Abacha ta yi magana a kan karairayin da ake yadawa a kan tsohon mijinta

Hajiya Maryam, matar tsohon shugaban kasa a mulkin soji, marigayi Janar Sani Abacha, ta ce abin kunya ne ake yi wa mamaci karya.

Maryam ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga labaran da ake yadawa a kan kudaden da ake dawowa Najeriya dasu, wadanda aka alakanta da mijinta

Yayin wata hira da aka yi da ita a Kano domin tunawa da cika shekaru 22 da mutuwar Abacha, Maryam ta ce da sannu gaskiya zata fito a kan kudaden da ake dorawa mijinta laifin sacewa.

Bazawarar ta zargi manyan mutanen Kano da cin amanar mijinta da ya mutu a shekarar 1998, "duk da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban jihar da kasa baki daya.

"Me yasa shi wannan mutum bai zama barawo ba sai bayan mutuwarsa?", kamar yadda Maryam ta tambaya.

Sannan ta cigaba da cewa, "sun ce an gano kudaden kuma ana dawo da su, nawa ne kudin da aka dawo da su bayan shekaru 22?

"Abin kunya ne ake yi wa mamaci karya, abin kunya ne ake yi wa shugaba karya.

"Idan ya aikata ba daidai ba, Allah ya sani. Idan wasu mutane ne ma suke yi masa sharri, lokaci zai nuna.

"Sai sun gurfana a kan gwuiwowinsu kamar yadda yanzu Amurka ta gurfana. Duk wani mugu sai ya durkushe kamar yadda annobar korona ta durkusar da dukkan duniya."

Hajiya Maryam ta bayyana marigayi Abacha a matsayin wanda ya taimaki mutane da dama.

Maryam Abacha ta yi magana a kan karairayin da ake yadawa a kan tsohon mijinta
Maryam Abacha
Asali: Facebook

"Ya yi aiki a Kano, sannan ya kafa Kanawa, akwai mutane da dama da ya taimaka amma yanzu, ba tare da wani dalili ba, ko gaisuwa bata shiga tsakanina da su

"Sun ma tsanemu. Amma me yasa? haramun ne yin hakan kuma Allah yana ganin kowa," kamar yadda Maryam ta bayyana.

DUBA WANNAN: Maiduguri: Mutum daya ya mutu, da dama sun raunata yayin mummunar arangama tsakanin Sojoji da kwamitin yaki da Korona

Tun bayar mutuwa Abacha a shekarar 1998 ake dawowa da Najeriya makudan kudaden da ya jibge a bankunan kasashen nahiyar Turai da Amurka, ya ajiye mafi yawancin kudaden ne da sunan 'ya'yansa.

Ko a cikin makon jiya sai da tsohon dogarin da ke kula da tsaron tsohon shugaban kasa Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya tashi ya sake kare mai gidansa a game da zargin da ake yi masa na satar dukiyar gwamnati.

Hamza Al-Mustapha ya ce gwamnatin Sani Abacha ta tuntubi sarakunan Arewa da na Kudu da duk wasu manya da ake ji da su a Najeriya kafin gwamnati ta boye biliyoyin kudin da yanzu ake kira ‘satar Abacha.’

Al-Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da gidan jaridar BBC Hausa, inda ya ce dole ta sa Janar Sani Abacha ya rika boye biliyoyin kudi a kasar waje domin ya hararo cewa za a makawa Najeriya takunkumi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel