Ranar damokaradiyya: Abubuwa 10 da Buhari ya yayi magana a kansu

Ranar damokaradiyya: Abubuwa 10 da Buhari ya yayi magana a kansu

A ranar Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga 'yan Najeriya don tunawa da ranar damokaradiyya ta 2020. Ya yi amfani da damar wurin bayyana ci gaban da aka samu a manyan sassa a fadin kasar nan.

Buhari ya ce mulkinsa ya samu manyan ci gaba duk da ci baya da aka samu a wasu sassan.

Ga abubuwa 10 da shugaban kasa ya lissafa a cikin jawabinsa:

1. An kammala titi mai tsawon kilomita 412 da ke Sukuk.

2. Kara hanyoyin yalwatar tattarin aziki ta noma da kiwo ba dogaro da man fetur ba kadai.

3. An yi amfanin da ya dace da kudaden da shugabannin da suka gabata suka wawure ta yadda ya dace.

4. Kokarin shawo kan rashin tsaro: An nakasa mayakan Boko Haram tare da durkusar da su.

5. Nasarar ciyar da yaran makaranta miliyan 10 da sauran al'amura na walwala da more rayuwa.

6. Manyan nasarori na samuwa a bangaren wutar lantarkin kasar nan.

7. Ilimi kyauta kuma na dole ga dukkan kananan yara a fadin kasar nan.

8. 'Yancin kafafen yada labarai: Gwamnatin Buhari ta tabbatar da 'yancin manema labarai a dukkan kasar nan.

9. Kokarin kawo karshen annobar korona wacce ta bullo kasar nan a watan Fabrairu na shekarar nan.

10. Ana gab da kammala gada ta biyu ta Neja wacce ta dade ana aikinta.

Ranar damokaradiyya: Abubuwa 10 da Buhari ya yayi magana a kansu
Ranar damokaradiyya: Abubuwa 10 da Buhari ya yayi magana a kansu. Hpto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

A wani labari na daban, hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari yana sallah yayin da yake zaune a kan kujera ya janyo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani.

An ci gaba da maganganun bayan ya yi sallar Idi a kan kujera a ranar 24 ga watan Mayun 2020 tare da yin sallar Juma'a a ranar 5 ga watan Yunin 2020 a gidan gwamnati da ke Abuja duk a kan kujera.

A dukkan lokutan, an ga shugaban kasar na zaune a kan kujera yayin da limamin masallacin fadar shugaban kasa, Abdul-Wahid Suleiman ke jan sallah raka'o'i biyu.

"Me hakan yake nufi?", daya daga cikin masu tsokaci mai suna Rasheedat Abdallah ta tambaya.

"A yayin sallar Idi, na ga shugaba Buhari a kan kujerar. Na sake ganinsa a kan kujerar yayin sallar Juma'a," ta kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel