An sallami wasu malaman BUK saboda IPPIS

An sallami wasu malaman BUK saboda IPPIS

Jami'ar Bayero da ke Kano, BUK, ta sallami wasu malamanta biyar da aka dauka wucin gadi saboda dokar gwamnati tarayya na shiga tsarin biyan albashi na IPPIS da bai bayar da daman daukan malamai na kwangila ba

Da ya ke tabbatar da lamarin, Shugaban BUK, Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya ce jami'ar ta ba wa malaman da abin ya shafa wa'adin kwanaki 40 a maimakon 30 kafin sallamarsu daga aiki.

Shugaban jami'ar ya ce an dauki matakin ne domin biyaya ga tsarin biyan albashi na IPPIS da ya ce a dena biyan malaman da aka dauka na wucin gadi a lokacin da ainihin malaman makarantan suka shiga tsarin na IPPIS.

An sallami wasu malaman BUK saboda IPPIS
An sallami wasu malaman BUK saboda IPPIS. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa hadimin Aisha Buhari rasuwa

"Yana daga cikin sharrudan shiga tsarin biyan albashi na IPPIS. Kuma gwamnatin tarayya ta fayyace mana cewa sai dai idan jami'ar za ta iya biyan su daga kudin shigar ta kuma a yanzu ba zamu iya biyansu ba," in ji shugaban.

Mr Yahuza Bello ya ce sallamar malaman na wucin gadi ba zai kawo cikas ga jami'ar ba duba da cewa tana da malamai kimanin 1,776.

Ya kara da cewa korar bai shafi ma'aikatan kwangilar da ba yan kasa ba.

Daya daga cikin malaman kwangilar da abin ya shafa, Dr Saidu Dukawa, tsohon shugaban Hukumar Hisbah ta Kano ya tabbatar wa jaridar Solacebase batun a ranar Alhamis.

Ya yi karin bayani cewa jami'ar ta sanar da shi cewa za dakatar da kwangilarsa na aikin koyarwa na shekaru bakwai domin dokar gwamnati na shiga tsarin biyan albashi na IPPIS.

Mr Dukuwa ya ce, "Na shafe shekaru bakwai ina aiki a matsayin ma'aikacin wucin gadi a kuma duk shekaru biyu ake sabunta kwangilar. Dama shekara mai zuwa za a sabunta kwangila amma an soke jiya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel