Kano: 'Yan sanda sun damke matasa 97 a gidan rawa

Kano: 'Yan sanda sun damke matasa 97 a gidan rawa

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke mutane 97 a kan laifin halarta gidan rawa tare da take dokar Jana walwala wacce aka saka don dakile yaduwar annobar korona a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya bayyana hakan a wata takarda d ya fitar a ranar Litinin a Kano.

DSP Haruna, ya bayyana cewa al'amarin ya faru ne a ranar 6 ga Yuni bayan bayanai da ta samu wurin karfe 1 na dare.

Ta tabbatar da cewa wasu jama'a na taro a wata otal mai suna Mozida da ke Sabo Garin jihar Kano.

Ya kara da cewa, bayan kwamishinan 'yan sandan jihar ya samu labari, ya tura jami'an tsaro da su damko masu karya dokar.

"Masu laifi 97 ne aka kama bayan sun take dokar nesa-nesa da juna yayin da dokar kulle ke aiki," yace.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce an kama mata 40 tare da maza 57 kuma an tuhumi manajan otal din.

Kano: 'Yan sanda sun damke matasa 97 a mashaya
Kano: 'Yan sanda sun damke matasa 97 a mashaya. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur

"An mika masu laifin gaban kotu don samun hukunci," ya kara da cewa.

A wani bangare na daban, rundunar ta damke wasu mutum biyu da take zargi da sokawa wani mutum mai suna Ibrahim Adamu almakashi a kirjinsa tare da kwace masa waya.

Haruna ya ce, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Yuni wurin karfe 3 na dare bayan sun balle gidan wanda suka kashe din a kwatas din Wailari da ke birnin Kano.

Ya yi bayanin cewa wadanda ake zargin sun soki mutumin da almakashi a kirji tare da ji mishi miyagun raunika.

"Bayan samun labari, mun tura mutanenmu inda lamarin ya faru sannan aka gaggauta mika mutumin asibitin kwararru na Murtala Muhammad don samun tallafin gaggawa.

"An kama wadanda ake zargin da almakashi da kuma adda," yace.

Haruna ya ce kwamishinan ya bada umarnin mika wadanda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka.

Za a mika su gaban kotu bayan an kammala bincike a kansu don karbar hukuncin da ya dace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel