Sallar Buhari a kan kujera ta janyo cece-kuce

Sallar Buhari a kan kujera ta janyo cece-kuce

Hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari yana sallah yayin da yake zaune a kan kujera ya janyo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani.

An ci gaba da maganganun bayan ya yi sallar Idi a kan kujera a ranar 24 ga watan Mayun 2020 tare da yin sallar Juma'a a ranar 5 ga watan Yunin 2020 a gidan gwamnati da ke Abuja duk a kan kujera.

A dukkan lokutan, an ga shugaban kasar na zaune a kan kujera yayin da limamin masallacin fadar shugaban kasa, Abdul-Wahid Suleiman ke jan sallah raka'o'i biyu.

"Me hakan yake nufi?", daya daga cikin masu tsokaci mai suna Rasheedat Abdallah ta tambaya.

"A yayin sallar Idi, na ga shugaba Buhari a kan kujerar. Na sake ganinsa a kan kujerar yayin sallar Juma'a," ta kara da cewa.

Wani mai tsokaci kuwa ya ce ya rasa me zai ce saboda daure masa kai da al'amarin ya yi.

Sallar Buhari a kan kujera ta janyo cece-kuce
Sallar Buhari a kan kujera ta janyo cece-kuce. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta

Amma kuma wasu sun ce babu wani aibu game da zamansa kan kujera yana sallah. Wasu sun zargi cewa akwai yuwuwar shugaban kasar na fama da ciwon baya ne.

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ki yin tsokaci a kan al'amarin.

Amma kuma wata majiya mai karfi daga fadar shugaban kasar ta ce babu wani aibu don tsoho ya yi sallah zaune a kan kujerar.

A yayin tsokaci a kan al'amarin, Ustaz Maisuna M. Yahaya, shugaban Al-Moustafiyya Islamic Society of Nigeria ya ce babu wani aibu game da hakan.

Ustaz ya kara da cewa, wajibcin tsayuwa ko zama ko kuma jingina a sallah ya danganta ne da lafiyar dan Adam.

Ya kara da cewa, Musulunci addini ne mai sauki don haka ba a amince mutum ya tsawwala ba bayan sauki ya zo a kowanne bangare.

A bangaren shekaru kuwa, 'yan Najeriya sun san cewa dattijo ne shugaban kasar ba yaro ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel