An fara damuwa kan yadda mutane 50 suka mutu a Jos cikin yan kwanaki

An fara damuwa kan yadda mutane 50 suka mutu a Jos cikin yan kwanaki

Hukumomi a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau sun nuna damuwarsu kan yadda ake samun yawaitar mace-mace cikin yan kwanakin nan ba tare da wani bayanannan dalili ba.

Adadin wadanda aka birne a makabartun karamar hukumar cikin kwanaki 20 da suka shude ya kai hamsin (50).

Majiya na kusa da makabarta mafi girma a garin, makabartar Zaria road, ya bayyana cewa adadin wadanda ake kai wa yanzu ya yi tashin gwauron zabo cikin yan mankonnin nan kuma akwai damuwa.

Wani mai hakar kabari yace, "bamu san abinda ya janyo mace-macen ba amma muna damuwa saboda adadin ya tashi cikin kwanakin nan."

"A makonni uku da suka gabata, adadin gawawwakin da muke birnewa ya ninka wanda mukeyi kafin yanzu."

"Da ranan nan kadai mun birne mutane biyar, da yiwuwan mu sake birne wasu (yau)."

Ya ce kimanin mutane 50 suka birne cikin makonni uku dasuka gabata.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An fara damuwa kan yadda mutane 50 suka mutu a Jos cikin yan kwanaki
An fara damuwa kan yadda mutane 50 suka mutu a Jos cikin yan kwanaki
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta yi murnan cika makonni biyu babu mai Korona a jihar

Shugaban karamar hukumar, Hanarabul Shehu Bala Usaman, ya tabbatar da labarin yawan mutuwar kuma ya bayyana matakin da suke dauka.

Ya bayyanawa jaridar Thisday cewa: "Labarin da kuka samu gaskiya ne; yanzu mun bude rijistan mace-mace a dukkan makabartun karamar hukumar."

"A da akwai ka'idar rijistan gawawwaki kafin birnesu amma yanzu mutane sun daina bin dokar."

"Abinda muke yi yanzu shine bude rijista a makabartu saboda an rattaba sunayensu kafin birnesu. Hakan zai bamu daman sanin ainihin abinda ke faruwa kafin mu iya tabbatar da cewa ana mutuwan da ya saba al'ada; wajibi ne mu sami hujjojin haka."

Game da cutar COVID-19, Usman ya ce karamar hukumar na iyakan kokarinta wajen wayar da kan al'umma gunduma-gunduma tunda lamarin ya zama haka.

Ya ce shugabancin karamar hukumar ba tayi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa yunkurin gwamnatin jihar dakile annobar.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa akalla kashi 60 daga cikin mace-macen jihar Kano na da alaka da annobar korona, jami'ai suka sanar.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a yayin bayanin inda aka kwana a gaban kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a ranar Litinin.

Jihar yankin arewa maso yamman ta fuskanci yawaitar mace-mace a jihar, kusan rayuka 979 da suka hada da na manyan sarakuna, ma'aikatan lafiya da manyan malamai.

Kamar yadda ministan yace, kashi 50 zuwa 60 na mace-macen na da alaka da cutar korona. Hakan yana nufin 490 zuwa 587 na mutanen da sukar rasu an gano cutar coronavirus ce ta kashesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel