Gwamnatin Jihar Borno ta dawo da gidajen Bama da ba a tare ba hannunta

Gwamnatin Jihar Borno ta dawo da gidajen Bama da ba a tare ba hannunta

A cikin farkon makon nan ne hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto cewa gwamnatin jihar Borno ta karbe wasu daga cikin gidajen da ke unguwar Indimi Estate.

Attajirin nan na jihar Borno, Alhaji Mohammed Indimi ne ya gina gidaje 100 a matsayin gudumuwarsa na taimakawa mutanen da Boko Haram su ka yi wa ta’adi.

Mohammed Indimi ya gina wadannan kananan gidaje ne domin samar da matsuguni ga wadanda ‘yan ta’addan Boko Haram su ka jikkata, su ka raba su da gidajensu.

A lokacin da mai girma gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara zuwa garin Bama, ya karbe gaba daya gidajen nan, inda ya sake bada su ga Bayin Allah masu bukata.

Gwamnan ya ce tun da wadannan mutane da aka ba gidajen ba su shiga ciki ba, ya nuna cewa ba su da bukata, don haka ya karbe gidajen daga hannunsu, ya mikawa wasu.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Mai magana da yawun bakin gwamnan, Malam Isa Gusau ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

“Gwamnatin jihar Borno ta karbe duka gidajen da aka raba a unguwar Indimi Estate.”

“Ba za mu yarda da yadda wasu za su yi ikirarin sun mallaki gidajen nan ba, amma su na zama a cikin garin Maiduguri.” Isa Gusau ya bayyana kalaman da gwamnan ya yi.

Yayin da ya ke garin Bama, gwamnan ya kai ziyara ta musamman ga mai martaba Sarki, inda ya sa ido wajen aikin raba kayan abinci ga mutane 25, 000 da su ke gudun hijira.

Gwamna Farfesa Zulum ya yi alkawarin cewa za a bude wasu makarantu a Bama, sannan kuma a dawo da mutanen yankin da su ke gudun hijira a sansanoni a kasar Kamaru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel