Allah kadai zai sakawa Abacha kan yadda ya sauya Najeriya - Al-Mustapha

Allah kadai zai sakawa Abacha kan yadda ya sauya Najeriya - Al-Mustapha

- Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana adadin kudin da Abacha ya barwa Najeriya lokacin da ya mutu

- Ya ce mutuwar marigayin babbar asara ce ga Najeriya musamman kan abubuwan da wadanda suka zo daga bayansa sukayi

Tsohon dogarin Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce Ubangiji kadai zai sakawa tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Marigayi Janar Sani Abacha, bisa namijin kokarin da yayi wajen sauya Najeriya.

Yayinda yake bukin shekara 22 da mutuwar Abacha ranar Litinin, Al-Mustapha ya ce mutuwar Abacha babbar rashi ce ga Najeriya kuma tarihi ba zata mantawa da abinda ya yiwa Najeriya ba.

A cewarsa, $200 million kadai Abacha ya samu cikin asusun ajiyar Najeriya na kasashen waje lokacin da ya hau mulki amma kafin mutuwarsa, ya samu nasarar karfafa tattalin arzikin Najeriya kuma ya bar $900,000 a asusun.

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya ce a lokacin Abacha, Dalar Amurka na N85 kuma babu hauhawar tattalin arziki ko kadan duk da kalubalen da kasar ke fuskanta.

Yace: "Allah kadai zai sakawa Janar Sani Abacha kan ayyukan kwarai da yayi wajen ganin ya sauya Najeriya,"

Alkaluma na sukan gwamnatin marigayi inda suke cewa shekaru 22 bayan mutuwarsa, har yanzu ana kwato kudaden da ya boye a kasashen waje.

Amma Al-Mustapha ya ce kawai wannan aikin wadansu yan tsiraru ne dake kokarin ganin cewa sun batawa maigidansa suna tare da boye ayyukan alkhairin da yayi.

KARANTA:1943-1998: Tarihin rayuwa da mulkin Marigayi Janar Sani Abacha a Najeriya

Ya kara da cewa tun mutuwar Abacha, daya daga cikin abubuwan da ke bakanta masa rai shine yadda shugaba Olusegun Obasanjo ya baiwa kasar Kamaru yankin Bakassi.

Ya ce tuni ya san akwai hadin baki da akeyi tsakanin wasu yan Najeriya da yan kasar waje dake kokarin kwacewa Najeriya yankin Bakassi mai dimbin arzikin man fetur.

"Da ni akayi yakin Bakassi na tsawon shekaru biyu cir. Ina sane da irin dimbin arzikin man fetur dake Bakassi kuma ya fi abinda ake samu yanzu a Najeriya yawa." Yace

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel