Zamfara: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'Dogo Dede' shugaban 'yan bindiga (Bidiyo)

Zamfara: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'Dogo Dede' shugaban 'yan bindiga (Bidiyo)

- Rundunar sojin Najeriya ta ci gaba da yi wa 'yan bindiga ruwan bama-bamai ta jiragen yaki a Zamfara

- Bayan rahoton sirri da dakarun sojin saman suka samu, sun kai wa 'yan bindiga farmaki har maboyarsu da ke dajin Kwayanbana

- Wannan harin ta jiragen yaki ya kawo mutuwar da yawa daga cikin 'yan bindigar tare dda tarwatsa maboyarsu

Rundunar sojin Najeriya ta ci gaba da yi wa 'yan bindiga ruwan wuta karkashin atisayen Operation Accord ta jiragen yaki.

A karkashin rundunar Operation Hadarin Daji, dakarun sojin saman Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga da ke dajin Kwayanbana a jihar Zamfara.

Dakarun sojin saman sun yi aiki ne da rahotannin sirri da suka samu wanda ya ce 'yan ta'addan na nan dankam a dajin tare da kogunan da ke kewayensa inda suka boye. A nan gagarumin dan bindiga mai suna Dogo Dede yake.

Hakazalika,sakamakon harin ta jiragen yaki da dakarun suka kai wa 'yan bindigar, an tarwatsa maboyarsu tare da halaka da yawa daga cikinsu.

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Daji a kan yadda suka nuna kwarewarsu.

Ya yi kira garesu da su ci gaba da aikinsu yadda ya dace tare da tabbatar da kawo karshen ta'addanci a yankin.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, hakimin kauyen Bagoni da limamin garin, duk sun mutu sakamakon harin tsakar dare da 'yan tawaye suka kai musu a jihar Taraba.

Mutum uku sun riga mu gidan gaskiya a kauyen Wurbo da ke karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu a ranar Juma'a a kauyen Tunga sakamakon harin ba-zata da 'yan ta'adda suka kai musu.

Kauyukan da aka kai wa hari duk na Jibawa ne; wani sassa na kabilar Jukun.

A yayin harin, an kone gidaje tare da dukiyoyin miliyoyin Naira da suka hada da amfanin gona wanda maharan suka yi awon gaba da su.

Wani mazaunin kauyen Bagoni wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce, Jibawa basu daga cikin rikicin da ke aukuwa tsakanin 'yan kabilar Tiv da Jukun a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel