Karin mutum 315 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 12,801

Karin mutum 315 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 12,801

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 315 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.41 na daren ranar Litinin 8 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 315 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos- 128

FCT-34

Rivers- 32

Edo- 28

Oyo- 22

Kaduna- 20

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Gombe- 13

Ogun- 8

Plateau- 5

Delta- 7

Kwara- 7

Kano- 5

Bauchi- 4

Katsina- 2

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Litinin 8 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 12801.

An sallami mutum 4040 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 361.

A wani labarin, kun ji cewa an tsinci gawar wani ɗan sanda mai muƙamin DSP tsirara a ɗakinsa da ke barikin ƴan sanda a ƙaramar hukumar Akwanga na jihar Nasarawa.

Ana zargin DSP Francis Onugha da ake yi wa laƙabi da (Dangote) ya mutu ne bayan kashe dare sun gasar lalata da budurwarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa, shine jami'i mai kula da sashin aikata laifuka (DCO) 1 na yankin Akwanga.

Wani ganau ba jiyau ba ya ce kofar dakin marigayin ɗan sandan a bude ta ke yayin da suka tsinci gawarsa da kumfa na fita daga bakinsa da hancinsa.

Ya yi iƙirarin cewa wata mata da ba a bayyana sunanta ba ta kwana a ɗakin ɗan sandan amma ta sulale ta fice bayan ta gano ya mutu.

Kakakin ƴan sandan jihar Nasarawa, ASP Nansel Rahman ya tabbatar da mutuwar DSP Onugha.

Sai dai ya musanta cewa mamacin ya rasu ne bayan gasar lalata da wata mata.

A cewarsa: "An kai gawar mamacin zuwa babban asibitin garin Akwanga inda za a bincika a gano sanadin mutuwarsa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel