Afrika ta Kudu da sauran kasashen Afrika 7 da tattalin arzikin Najeriya ya doke nasu a bana
- Najeriya ta sha gaban sauran kasashen nahiyar Afrika a kididdigar karfin tattalin arziki a shekarar 2019
- An yi kiyasin cewa karfin tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2019 ya kai darajar dalar Amurka biliyan $444.916
- Kasar Afrika ta Kudu ta dawo mataki na biyu da darajar karfin arzikin da ya kai dala biliyan $371.298
Kididdigar karfin tattalin arzikin kasashen nahiyar Afrika na shekarar 2019 ya nuna cewa karfin tattalin arzikin Najeriya ya doke na kasar Afrika ta Kudu da wasu sauran kasashen nahiyar Afrika ma su karfin tattalin arziki.
Kiyasin ya nuna cewa karfin tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2019 ya kai darajar dalar Amurka biliyan $444.916.
Kasar Afrika ta Kudu ta dawo mataki na biyu da kiyasin karfin tattalin arzikin da ya kai dalar Amurka biliyan $371.298, sai kuma kasar Masar a mataki na uku da kiyasin tattalin arzikin da ya kai dalar Amurka biliyan $299.589.
Kasashen Afrika da suka hada da Algeria, Angola da Morocco sun zo a mataki na hudu, bakwai da biyar, kmar yadda kididdigar da 'Afrika fact zone' ta gudanar.
A cikin wani sako da 'Afrika Fact zone' ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu, ta lissafa kasashen Afrika 8 mafi karfin tattalin arziki a shekarar 2019 kamar haka;
1. Nigeria ($444.916 billion)
2. South Africa ($371.298 billion)
3. Egypt ($299.589 billion
4. Algeria ($183.687 billion
5. Morocco ($121.350 billion)
6. Kenya ($99.246 billion)
7. Angola ($92.191 billion)
8. Ethiopia ($90.968 billion)
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin shugaba mai hangen nesa da ke iya ganin gobe.
A cewar gwamnan, hangen nesa ne yasa shugaba Buhari ya bawa harkar noma fifiko tun bayan hawansa mulkin Najeriya a shekaru biyar da suka gabata.
El-Rufa'i ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin kaddamar da shirin gwamnatin tarayya na rabawa manoma irin noma a jihar Kaduna.
DUBA WANNAN: FG ta bayyana matsayin Buhari a kan makomar 'yan N-Power da aka fara dauka
A karkashin shirin raba irin noma ga manoma a fadin Najeriya, ma'aikatar harkokin noma da raya karkara ta kaddamar da rabon irin noma ga manoman jihar Kaduna
Ministan harkokin noma da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono, ne ya kasance jagora yayin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya kasance babban bako mai gabatar da jawabi a wurin taron.
"A yanzu haka kasarmu ta hau hanyar cimma wadatuwa a bangaren abincin da muke nomawa a gida kamar su shinkafa, masara da sauransu," a cewar El-Rufa'i.
Gwamnan ya kara da cewa da yanzu 'yan Najeriya sun shiga halin ni 'yasu ba don hangen nesa na shugaba Buhari wajen hana shigo da kayan abinci ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng