Buhari ya aike wa 'yan bindiga sako mai girgiza zuciya

Buhari ya aike wa 'yan bindiga sako mai girgiza zuciya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja kunnen 'yan bindiga a kan su yada makamai ko kuma su fuskanci mummunan karshe mai cike da tozarci.

Shugaba Buhari ya bada wannan jan kunnen ne a daren Alhamis yayin taro a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja tare da Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

A takardar da shugaban kasar ya bai wa manema labarai a ranar Asabar ta hannun Garba Shehu, ya ce shugaban kasar ya tabbatar da cewa 'yan bindigar da suka kashe rayukan da basu taka musu ba, ba za a taba sassauta musu ba.

Ya ce za a dauka matakai masu tsauri ta hannun dakarun sojin kasar nan a kan 'yan bindigar da ke jihohin Zamfara, Sokoto, Neja, Katsina da Kaduna.

Ya tabbatar wa da jama'a tare da gwamnatin jihar Katsina cewa an sake tsananta tsaro tare da sabunta atisayen rundunar soji don inganta tsaron rayuka da kadarori a jihar da sauran sassan kasar nan.

Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen jajanta wa Gwamna Masari rashin rayukan da aka yi a jihar Katsina sakamakon harin 'yan bindiga.

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya yi ta'aziyyar hakimin Yantumaki, Atiku Maidabino da kuma shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani Duburawa.

A wani labari na daban, hakimin kauyen Bagoni da limamin garin, duk sun mutu sakamakon harin tsakar dare da 'yan tawaye suka kai musu a jihar Taraba.

Mutum uku sun riga mu gidan gaskiya a kauyen Wurbo da ke karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu a ranar Juma'a a kauyen Tunga sakamakon harin ba-zata da 'yan ta'adda suka kai musu.

Kauyukan da aka kai wa hari duk na Jibawa ne; wani sassa na kabilar Jukun. A yayin harin, an kone gidaje tare da dukiyoyin miliyoyin Naira da suka hada da amfanin gona wanda maharan suka yi awon gaba da su.

Wani mazaunin kauyen Bagoni wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce, Jibawa basu daga cikin rikicin da ke aukuwa tsakanin 'yan kabilar Tiv da Jukun a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel