Magidanci ya yanke jiki ya fadi bayan gama zina da matar aure da ya gayyato gidansa (Bidiyo)

Magidanci ya yanke jiki ya fadi bayan gama zina da matar aure da ya gayyato gidansa (Bidiyo)

Wata matar aure da ba a bayyana sunanta ba ta jefa kanta cikin mawuyacin hali bayan ta ziyarci magidanci a gidansa.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da ke da aure ya yanke jiki ya fadi bayan sun gama zina.

Amma matar ta musanta cewa tana da hannu cikin abinda ya faru kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ta ce ba ta san dalilin da yasa mutumin ya yanke jiki ya fadi ba inda ta nuna ta yi nadamar barin yayanta a gida domin zuwa tayi zina da shi sai kuma gashi ya yanke jiki ya fadi bayan sun gama.

Ta kuma roki mutanen da suka zo taimakawa mutumin su kyale ta ta tafi gida domin ta kula da yayan ta da ta bari.

Daga bisani an garzaya da magidancin asibiti a kan babur.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa.

DUBA WANNAN Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kama wani matashi, Ishaku mai shekaru 21 da haihuwa saboda kashe abokinsa, Zeloti ta hanyar daba masa wuka don rikici a kan budurwa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani mashaya a garin Dass a ranar Juma'a 29 ga watan Mayu inda Ishaku ya caka wa Zeloti wuka har sau uku kan musun da suke yi a kan wanene ainihin saurayin yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Wakili ya ce an garzaya da Zeloti John zuwa babban asibitin garin Dass inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

An birne shi a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2020.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin kuma yana tsare yayinda ake cigaba da binciken gano musababbin mutuwar mammacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel