Karin mutum 350 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 11516

Karin mutum 350 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 11516

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 350 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.43 na daren ranar Alhamis 4 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 350 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-102

Ogun-34

FCT-29

Borno-26

Kaduna-23

Rivers-21

Ebonyi-17

Kwara -16

Katsina-14

Edo-10

Delta-10

Kano-10

Bauchi-10

Bayelsa-9

Imo-8

Plateau-4

Ondo-3

Nasarawa-2

Gombe-1

Oyo-1

DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Alhamis 4 ga Yuni 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 11516.

An sallami mutum 3535 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 323.

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kama wani matashi, Ishaku mai shekaru 21 da haihuwa saboda kashe abokinsa, Zeloti ta hanyar daba masa wuka don rikici a kan budurwa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani mashaya a garin Dass a ranar Juma'a 29 ga watan Mayu inda Ishaku ya caka wa Zeloti wuka har sau uku kan musun da suke yi a kan wanene ainihin saurayin yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Wakili ya ce an garzaya da Zeloti John zuwa babban asibitin garin Dass inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

An birne shi a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2020.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin kuma yana tsare yayinda ake cigaba da binciken gano musababbin mutuwar mammacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel