COVID-19: Nan da makonni kadan korona za ta yi kaura daga Kano - Jami'ai

COVID-19: Nan da makonni kadan korona za ta yi kaura daga Kano - Jami'ai

Shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta jihar Kano, Dr Tijjani Hussein, ya bayyana cewa makonni kadan suka rage cutar ta yi kaura daga jihar Kano.

Hussein, wanda ya bayyana hakan a yayin tattaunawa a kan inda aka kwana a kan cutar a jihar Kano a ranar Alhamis, ya yi kira ga mazauna jihar da su dauka matakan dakile yaduwar cutar.

Ya ce: "Idan mazauna jihar Kano za su kiyaye dokokin wanke hannu, saka takunkumin fuska da kuma nesa-nesa da juna, ina tabbatar da cewa nan da makonni kalilan za a nemi korona a Kano a rasa."

Shugaban kwamitin ya kara da cewa, dukkan masu cutar da aka samu an samo su ne daga kananan hukumomi 30 na jihar amma kuma kashi 90% daga cikin masu cutar 'yan birnin Kano ne.

Ya kara da cewa, kashi 76 na masu cutar a jihar maza ne inda kashi 24 suka kasance mata.

A martanin gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya ce sannu a hankali jihar ke koyon komawa walwalarta duk da cutar.

Ya ce: "Da farko muna kallon lamarin a matsayin sabon abu wanda bamu taba sani ba. Amma a halin yanzu, mun san hanyar kamuwa da cutar da kuma hanyar kare kai."

"Mun san hanyar wanke hannaye, nesa-nesa da juna da kuma saka takunkumin fuska. Idan muka ci gaba da bin doka, za mu kawo karshen annobar a Kano," ya kara da cewa.

COVID-19: Nan da makonni kadan korona za ta bar Kano - Jami'ai
COVID-19: Nan da makonni kadan korona za ta bar Kano - Jami'ai. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu cif a jihar sakamakon annobar korona.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne a lafiya yayin taro da kwamitin yaki da cutar na jihar ta gudanar.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, cike da alhini yake sanar da mutuwar mutum hudu wanda suka hada da dan majalisar jihar mai wakiltar Nasarawa ta yamma daga cikin mutum 90 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, samfur 705 aka kai wa hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya tun bayan da aka fara gwajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel