Zulaihatu Nasir ta yiwa kishiyarta wanka da tafasasshen ruwan zafi a Kano

Zulaihatu Nasir ta yiwa kishiyarta wanka da tafasasshen ruwan zafi a Kano

Wata uwargida yar shekara 26 a unguwar Zango dake birnin Kano, Zulaihat Nasir, ta jiwa kishiyarta, Nafisa Isa, mumunan rauni bayan yi mata wanka da ruwan zafi.

A labarin da Jaridar Daily Trust ta ruwaito, Nafisa da Zulaihat na zaman aure ne gidan Ibrahim Sabo, mazaunin jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa wacce aka watsawa ruwan zafin ta ji raunin kuna a kai da kirhi kuma an garzaya da ita asibitin Abdullahi Wase.

KU KARANTA: Asibitin ABUTH Shika ta fara cika da masu cutar Korona - Masarautar Zazzau ta koka

Zulaihatu wacce ta aikata wannan laifi ta yi bayani a ofishin yan sanda cewa kishiyarta ce ta fara kulleta cikin daki kuma tayi barazanar banka mata wuta.

Ta ce ta yi mata wanka da ruwan zafi ne matsayinramuwar gayya kan kulleta da barazanar da tayi mata.

Tace: "Mun yi fada da ita ne, amma da na koma dakina na, sai ta kulle kofar ta garkameni ciki tana barazanar banka min wuta cikin dakin."

"Tun karfe 4 na yamma da ke kulle ni cikin dakin har Magariba da Maigidanmu ya dawo gida."

"Saboda haka na fusata kuma na yanke shawarar daukar fansa ta hanyar zuba mata ruwan zafi."

Amma yayinda jami'an yan sanda ke yi mata tambayoyi, ta bayyana nadamarta kan abinda ta aikata.

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Harina Kiyawa, wanda ya tabbatar da labarin ya ce ya faru ne ranar Lahadi, 31 ga Mayu misalin karfe 11 na safe.

Ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Habu Sani, ya bada umurnin mayar da lamarinta ofishin sashen CID domin bincike mai zirfi.

Ya kara da cewa idan aka kammala binciken, za a caji duk wanda aka kama da laifi zuwa kotu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel