Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sassauta dokar zaman gida a Kano

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin sassauta dokar zaman gida a Kano

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin fadar shugaban kasa kan yakar cutar COVID-19 wato PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar.

Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, sun gana da shugaba Buhari ranar Lahadi,kuma sun bashi shawari kan matakan da za'a dauka gaba.

Bayan ganawar, Shugaban kasa ya amince da sassauta dokar hana fita a jihar Kano.

A hirar kwamitin da manema labarai ranar Litinin, 1 ga Yuni, Boss Mustapha, ya sanar da hakan ga daukacin mutan jihar Kano.

Yace: "PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020."

"Za'a cigaba da taimakawa gwamnatocin jihar wajen tabbatar da cewa su zasu cigaba da gudanar da aikin aiwatar da shawari da dokokin da kwamitin PTF ta gindaya."

"Hukumar NCDC za ta cigaba da baiwa jihohi gudunmuwa ta hanyar basu shawari musamman kananan hukumomin da aiki yayi yawa."

"An sassauta dokar hana fita a jihar Kano."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur a fadin Najeriya zuwa N121.50 ga lita sabanin N125.00 da ake sayarwa yanzu

A bangare guda, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da Majami'u kadai) da kasuwanni a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.

Yace: "PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020."

"An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi."

"Za'a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel