Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur zuwa N121.50

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur zuwa N121.50

Gwamnatin tarayya ta rage farashin litan mai a fadin Najeriya zuwa N121.50 sabanin N125.00 da ake sayarwa yanzu.

Hukumar duba farashin man fetur PPPRA ta yi sanarwa ne a wasikar da ta aikewa yan kasuwar mai a ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

Daily Trust ta ruwaito cewa an rage farashin man feturin ne sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da annobar COVID-19 ta haifar.

Wannan shine karo na uku da za'a rage farashin man fetur cikin wannan shekara ta 2020.

A ranar 18 ga Maris, gwamnatin tarayya ta sanar da ragin farashin litan mai daga N145 zuwa N125. Daga baya a ranar 31 ga Maris, an sanar da karin ragi daga N123.50 zuwa N125.00.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur zuwa N121.50
Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur zuwa N121.50
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta bukaci kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta rage farashin zuwa N123 a watan Mayu da ya gabata, yan kasuwar mai da gidajen mai basu rage farashin ba, N125 suka cigaba da sayarwa.

Yan Najeriya na tsoron da yiwuwan yan kasuwan mai su kara kunnen kashi ga wannan ragi kamar yadda sukayi a watan jiya.

Farashin danyen man fetur ya yi fadin da ba a taba tsammani ba yayinda cutar Korona ta addabi duniya.

Kawo yau, farashin gangar danyen man fetur a kasuwar OPEC $29.4 ne. Kuma sanannen abu ne cewa idan farashin mai ya ragu a kasuwar duniya, kudin tacaccen mai zai ragu a nan gida Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel