'Yan bindiga sun kashe hakimin 'Yantumaki a Katsina

'Yan bindiga sun kashe hakimin 'Yantumaki a Katsina

Wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun harbe hakimin 'Yantumaki har lahira a jihar Katsina, Abubakar Atiku Maidabino a fadarsa a safiyar ranar Litinin.

Wata majiya daga garin ta shaidawa Daily Trust cewa 'yan bindigan sun taho a babura ne misalin karfe 12 na dare inda suka rika harbe harbe a iska domin razana mutanen kauyen.

Daga bisani yan bindigan sun shiga cikin fadar suka kashe hakimin nan take kuma suka raunata daya daga cikin masu gadinsa.

Za a yi janai'zar mammacin misalin karfe 11 na safe a fadarsa bisa koyarwan addinin musulunci.

'Yan bindiga sun kashe hakimin 'Yantumaki a Katsina
'Yan bindiga sun kashe hakimin 'Yantumaki a Katsina. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da harin tare da kashe hakimin.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sabbin direktoci 6 da Buhari ya nada a NNPC

A wani rahoton, mun kawo muku cewa 'yan bindiga a ranar Asabar sun sace dan kasuwa, Yusuf Maifata a gidansa da ke garin Sankara da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Mazauna unguwar sun ce yan bindigan sun isa unguwar ne misalin karfe 1.47 na dare dauke da bindigu suna harbe harbe wadda hakan ya sa mutane suka firgita sannan suka sace Maifata daga gidansa.

Wani daga cikin iyalan dan kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "Maifata ya dade yana fama da rashin lafiya. An sallamo shi daga asibiti ranar Alhamis yana murmurewa a gida ne sai kwatsam abin ya faru."

Majiyar ya kuma bayyana cewa yan bindigan sun kira iyalansa sun nemi a biya su Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa.

Sun kuma tambayi irin abincin da dan kasuwan ya saba ci da magungunan da asibiti suka rubuta masa ya rika sha.

Yana sume suka tafi da shi saboda firgicin karar harbin bindiga da ya rika ji yayin da ya ke kwance a gadonsa kafin su shiga gidan su dauke shi kamar yadda majiyar ya shaidawa Premium Times.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa, Audu Jinjiri ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Mr Jinjiri ya ce tuni rundunar ta baza jamianta na sashin yaki da masu fashi da makami da garkuwa da mutane su bi sahun yan bindigan domin ceto dan kasuwan mai shekaru 75 da haihuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel