Karin mutum 553 sun harbu da korona a Najeriya, jimilla 9855

Karin mutum 553 sun harbu da korona a Najeriya, jimilla 9855

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 553 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.55 na daren ranar Asabar, 30 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 553 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-378

FCT-52

Delta-23

Edo-22

Rivers-14

Ogun-13

Kaduna-12

DUBA WANNAN: Katsina: Mutum 13 sun mutu yayin da mutanen gari suka fafata ta 'yan bindiga

Kano-9

Borno-7

Katsina-6

Jigawa-5

Oyo-5

Yobe-3

Plateau-3

Osun-1

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 9855.

An sallami mutum 2856 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 273.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel