Katsina: Mutum 13 sun mutu yayin da mutanen gari suka fafata ta 'yan bindiga

Katsina: Mutum 13 sun mutu yayin da mutanen gari suka fafata ta 'yan bindiga

Mutane 13 ne suka mutu yayin da mutanen gari suka fafata da barayin shanu a arewacin Najeriya inda lamarin ke karuwa a yankin kamar yadda 'yan sanda suka ce a ranar Asabar.

Mazauna kauyuka hudu ne suka hada kansu inda suka tunkari barayin shanun kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan jihar Katsina Gamba Isah ya ce.

"Mutane 13 sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata," in ji Isah.

"Mun dade muna fada wa mutanen da ke dauke da adduna da bindigun mafarauta su dena tunkarar 'yan bindiga da suke zuwa da bindigun zamani," a cewar Isah.

Katsina: Mutum 13 sun mutu yayin da mutanen gari suka fafata ta 'yan bindiga
Katsina: Mutum 13 sun mutu yayin da mutanen gari suka fafata ta 'yan bindiga. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN Birai sun gudu da kayan gwajin COVID-19 bayan kai wa ma'aikacin lafiya hari

'Yan bindiga sun dade suna cin karensu babu babbaka a jihohin arewa maso yamma, akwai kuma rikici na fili da hare-hare na yan daba da wasu miyagu.

Satar shanu da garkuwa domin karbar kudin fansa yana bunkasa ne a lokacin da aka samu karancin tsaro.

Rundunar sojin Najeriya ta kai hare haren da jiragen yaki a sansanin yan bindiga a Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari da jihohin Zamfara da ke makwabtaka da ita domin kawo karshe haren haren.

Kimanin mutane 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya a cikin makon nan.

Kungiyar International Crisis Group a satin da ta gabata ta yi gargadin cewa kungiyoyi masu jihadi da suka kwashe shekaru goma suna tayar da kayan baya a arewacin Najeriya suna kara karfi.

Masu binciken mazauna Brussels sun ce akwai yiwuwar yankin ya zama matattara masu yaki da sunan yada musulunci a yankin Sahel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel