Matar aure ta zazzabga wa miji mari bayan ta kama shi budurwa a wurin cin abinci (Bidiyo)

Matar aure ta zazzabga wa miji mari bayan ta kama shi budurwa a wurin cin abinci (Bidiyo)

- Wani bidiyon fusatacciyar mata da ta kama mijinta da wata ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

- A bidiyon, matar aure ce ta dinga zabga wa mijinta mari bayan kama shi da tayi da budurwa a wurin cin abinci

- Bata tsaya nan ba, ta watsa masa miyar abincin da ya siya tare da tabbatar masa da cewa za su hadu a gida

A wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ga wata mata ta fada mijinta da duka bayan ta kama shi da wata a wurin cin abinci.

Bidiyon ya jawo cece-kuce daga jama'a wadanda suka ganshi.

Fusatacciyar matar ta kasa jure ganin mijinta da wata mata. Hakan ne yasa ta zazzabga masa mari masu matukar kara a fuskarsa.

Ta tambayeshi ta yadda ya samu kwarin guiwar da har ya fara mu'amala da wata mace bayan tana nan da ranta.

Bata tsaya a nan ba, ta watsa wa mijin miyar abincin da ya siya a gidan cin abincin tare da tabbatar mishi da cewa za su hadu a gida.

A nan take ta juya tare da ficewa daga gidan cin abincin.

Masu kallo sun sha matukar mamaki tare da tambayar magidancin yadda ya auri masifaffiyar mata haka.

Sun ci gaba da yi mata tofin Allah-wadai game da wannan mummunar dabia'a da ta bayyana.

KU KARANTA: Gagaruman nasarori 3 da Buhari ya samu cikin shekaru 5 - Fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, bayan rufe Masallatai na sama da watanni biyu, ma'aikatar al'amuran addinin Musulunci ta yi kira ga ma'aikatanta da su fara gyara da tsaftace manya da kananan Masallatai sama da 90,000 a masarautar.

Za a bude Masallatan ne a ranar Lahadi mai zuwa amma banda Masallatan garin Makkah a wannan budewar.

Kamar yadda rahoton Saudi Gazette ya bayyana, za a bude Masallatan ne kamar yadda umarnin Ministan al'amuran addinin Musulunci, Dr. Abdullatif Al-Sheikh da kuma shawarwarin majalisar manyan malamai ta bayyana.

Ma'aikatar na yakin wayar da kai a kafafen yada labarai, Talabijin, rediyo, jaridu da sauran kafafen yada labarai.

Ana wannan wayar da kan ne don kiyaye hanyoyin yaduwar cutar ko bayan budewar Masallatai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel